Kungiyar Kwadago ta kasa ta baiwa Shugaba Muhammad Buhari wa'adin zuwa karshen watan Disamba kan ya fara biyan sabon albashi mafi karanci na 30,000.
Haka ma, kungiyar ta yi gargadin cewa idan har gwamnati ta rage Wani abu daga cikin 30,000 din, kungiyar za ta dauki mataki. Har yanzu dai, Buhari bai mikawa majalisar tarayya rahoton karin albashin ba don amincewar majalisar ba.

No comments