5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 HUKUMAR KWASTAN TA YI BABBAN KAMU - Arew@Blog HUKUMAR KWASTAN TA YI BABBAN KAMU - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

HUKUMAR KWASTAN TA YI BABBAN KAMU



...sun kama harsashai sama da dubu hudu

Babban kwanturola na kwastom Zone C, Mr Kayode Olusemire jiya Talata ya kira taron manema labarai, ya bayyana cewa jami'an kwastom da suke sintiri sun samu nasaran kama harsashin bindiga guda dubu hudu da dari uku da saba'in da biyar (4,375) da haramtaccen maganin kodin (codeine) guda dubu daya da dari daya da sittin (,1,160), rigunan sojoji guda 200, buhunan shinkafa guda (430), kwali dauke da kwayoyin turamol (tramadol) guda 300,


Mr. Kayode Olusemire, yace sun kama mutum uku, kuma da zaran an kammala bincike za'a gabatar dasu a kotu, ya kara da cewa harsashin bindigar an kama ne a garin Enugu, sannan shinkafar sun kama a tsakanin hanyar Port-Harcourt da Aba, kayan sojojin kuma an kama a garin Onitsha jihar Anambra


Yace abin takaici ne yadda wasu gurbatattun mutane suke kokarin shigo da haramtattun abubuwa cikin Nigeria domin su dinga aikata miyagun laifuka duk da kokarin da jami'an tsaron kwastom suke wajen dakilesu

Muna rokon Allah Ya cigaba da tona musu asiri

No comments

Powered by Blogger.