IShin Da Gaske Ne Sergio Ramos Ya Sha Kwaya
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta karayata rahoton da wata jarida a kasar Jamus ta wallafa inda tace dan wasan baya na kungiyar yaki zuwa ayi masa gwajin da a keyiwa ‘yan wasa agane cewa sunsha kwaya ko basu sha ba. A na zargin dai lamarin yafaru ne a
shekarar da Real Madrid ta doke kungiyar kwallon kafa ta Jubentus a wasan zakarun nahiyar turai da aka buga a birnin Cardiff na kasar Wales inda masu gwajin suka gayyaci Ramos shi kuma yaki zuwa.
Ana zargin Ramos dai da shan wata kwaya mai suna Dedemethone wadda take kara kuzari a wasan da Real Madrid din tasamu nasara akan Jubentus daci 4-1wasan da dan wasa Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu. “Ramos bai karya doka ba kuma hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai ta bukaci mu basu karin bayani akan abinda yafaru kuma mun basu sannan kwamitin gwajin kwayar ya tabbatar da cewa mun bada bayani” a wata sanarwa da Real Madrid ta fitar a shafinta na yanar gizo Kungiyar Real Madrid tace bayanin da wannan jarida ta wallafa karya ne kuma ba gaskiya bane saboda dokar hukumar bai hana ‘yan wasa shan kwayar da akace yasha ba kuma sun bayar da bayani yadda yakamata.
Sai dai rahoton jaridar ya bayyana cewa laifin hukumar kwallon kafar nahiyar turai ne bayar da damar shan kwayar a wasan hakan yasa sukaki yin bincike akan maganar amma tabbas Ramos yasha kwayar.

No comments