Yau Ake Nada Atiku A Matsayin Wazirin Adamawa
A yau Lahadi ake nada dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a matsayin Wazirin Adamawa, Atikun zai zama shine Wazirin Adamawa na bakwai. Tsofaffin gwamnoni,
Sarakunan gargajiya, shugabannin addini, da manyan jami’an siyasa, manyan ‘yan kasuwa da manyan baki daga kasashen ketare ne suka halarci bikin a garin Yola dake jihar Adamawa
Tsohon gwamnan jihar Adamawa Bala Ngilari, tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso, da ‘yan kungiyar shi ta Kwankwasiyya sun kawata wajen bikin da jajjayen
hulunan su na kwankwasiyya. Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, shugaban majalisar dattawa,
Bukola Saraki, tsohuwar ministar mata, Aisha Alhassan, Sanata Ben Obi, su ma duk sun halarci taron.

No comments