Akwai yiwuwar baiwa 'yan Road Safety makamai
Gwamnatin tarayya tace zata duba yiyuwar amincewa da baiwa hukumar nan ta FRSC damar rike makamai.
Hukumar tana bukatar a bata wannan dama inda har ta tanadi wajen ajjiye makaman nata a wani waje a jihar Abuja.
Mai magana da yawun hukumar yace ba wani abu bane dan an basu wannan dama tunda sun daura damarar yaki ga masu take doka
Mai magana da yawun hukumar Bisi Kazeem yace ba wani abun tur bane idan an amincewa hukumar daukar makamai duba da cewa sun daura damarar yaki ga masu son karya doka.
A shekara ta 2016 ma'aikatan hukumar sun rasa rayukan su a dalilin yan fashi ko kuma diribobin dake son gujewa ma'aikatan.Wanda wannan ya sanya hukumar take tunanin nemawa ma'aikatan ta kariya.

No comments