El Rufa'i Za Mu Zaba A 2019 - Kungiyar Karuwai (ASHAWO) Ta Jihar Kaduna
Kungiyar Mata Karuwai ta jihar kaduna ” Association of Commercial Sex Workers ” sun yabawa gwamna jihar kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, bisa dage Dokar takaita Zirga-zirga a cikin Garin kaduna inda suka yi masa alkawarin zabensa a zaben shekarar 2019 Mai zuwa.
Kungiyar tace ya zama wajibi su yabawa gwamnan bisa irin Matakan da ya dauka wajen samar da zaman lafiya a jihar.
Shugaban kungiyar Justina Emmanuel, ita ce ta bayyana haka a zantawarta da manema labarai a kaduna, inda tace dage Dokar da gwamnan yayi zai taimaka musu wajen Kara samun kudadan Shiga musamman ganin cewa kasuwarsu ta dare ce.
Akan Hakan, Kungiyar tace gwamna El-Rufa’i shine Dan takarar su na kujerar gwamna a jihar kaduna.
Justina, ta Kara da cewa rikicin kaduna ya kawo musu cikas wajen na Rashin samun kwastomomi. Tace sun samu Rashin kwastomomi a Tituna Waff da Rabah da unguwannin Narayi da Barnawa da dai sauran su inda suka ce yanzu hada-hadar su zata dawo Kamar kullum.
Shugabar tace kwanakin da akayi na Rashin yawon dare ya haifar musu da talauci da kuncin rayuwa, amma da taimakon El Rufa'i acewarsu, yanzu zasu farfado.

No comments