5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 GANDUJE YA CI RASHAWA A TSIGE SHI KAWAI, Cewar Dr. Ahmad Gumi - Arew@Blog GANDUJE YA CI RASHAWA A TSIGE SHI KAWAI, Cewar Dr. Ahmad Gumi - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

GANDUJE YA CI RASHAWA A TSIGE SHI KAWAI, Cewar Dr. Ahmad Gumi



Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Fitacen malamin addinin islama dake garin Kaduna Sheikh Dakta Ahmad Gumi ya yi kira da mahukunta da su tsige gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje bisa zarginsa da karbar rashawa.

Shehin malamin ya yi wannan jawabi ne jiya Alhamis game da kudin rashawa da aka kama gwamna Ganduje yana karba.

Malam ya nuna bambanci dake tsakanin kudin da gwamnoni suke canzawa daga wani aiki zuwa wani aiki da kuma karkatar da dukiyar al'umma da cinye ta da suke yi da bambanci tsakanin wanda zai karbi kudi domin ya bada wata kwangila.

Idan kana kare musulunci ne to ka bi abinda musulunci ya ce, idan kuwa kana kare siyasa ne to ka sani siyasar za ta barka a duniya addini ya raka ka lahirarka.

No comments

Powered by Blogger.