A CETO 'YAN BIYUN ZAMFARA DA SAURAN
Daga Fauziyya D. Sulaiman
A jiya wani babban Dan jarida ya aiko min da hirar da aka yi da wanda suka yi garkuwar da Yan biyu, hankali na ya yi matukar tashi jin halin da yaran ke ciki, sai dai kafin na samu damar turawa, mu nemi taimakon jama'a ya Kara turo min wani bayanin da cewar, Gwabnan Zamfara ya biya kudin, wajan karfe sha biyun dare ya turo min, tsananin farin ciki ya sa ni sanar da jama'a a daran.
Sai dai ina kunna wayata da safe na fara ganin kira da sakwanni akan ba haka abin ya ke ba, Gwabnan Zamfara bai ce komai ba har yanzu akan lamarin, Sarkin Kano Alhaji Muhammad Sunusi 2, shine kawai Wanda ya saka baki cikin lamarin, na kira Danjaridar ya ce tun jiya ya Kira ni domin ya tabbatar min da labarin ba haka ya ke ba, wanda suka sanar da shi sun tabbatar an sami akasi a labarin, ya kira ya sanar da ni amma wayata a kashe.
Cikin gaggawa mu ka nemi Karin bayani daga Mai Martaba Sarki ta gurin Haj. Sa'adatu Baba, inda muka samu bayani Kai tsaye daga bakin Mai Martaba Sarkin Kano.
Ya ce "Tabbas an sanar da shi maganar yaran, kuma ba su kadai ba ne, wajan mutum Saba'in masu garkuwar suka kwashe, nan take kuma suka yi magana da fadar shugan kasa, fadar shugaban kasa kuma suka yi magana da Gwabnan Zamfara da jami'in tsaro, ya kuma tabbatar mana da Insha Allahu za su yi iyakacin kokarin su don ganin an karbo su" shine abin da Sarki ya sanar da mu.
Babban tashin hankalin shine, har cikin Unguwa aka shiga aka kwashe yan biyun da wasu matanen kusan Saba'in, Wanda an ce hakan ba sabon abu ba ne a jihar, fitar wannan labarin na 'Yan biyu ne ya saka jama'a suka san halin da Jahar ke ciki.
Don haka muna kira ga Gwabnatin Zamfara da fadar shugaban kasa, da su yi duk mai yuwuwa domin daukar mataki akan masu garkuwa da mutane, musamman na Jahar Zamfara, sannan su kwato mana yan biyu da sauran jama'ar da aka yi garkuwar da su.
Daga karshe muna godiya ga Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammad Sunusi, kasancewar duk fadin Arewa shine mutamin da ya saurari kukan mu akan wadannan yara, Allah ya karawa Sarki lafiya, ya kubutar da wadanann bayin Allah. Amin.

No comments