5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Kungiyoyin kwadago za su fara yajin aiki a Najeriya - Arew@Blog Kungiyoyin kwadago za su fara yajin aiki a Najeriya - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Kungiyoyin kwadago za su fara yajin aiki a Najeriya

Kungiyoyin Kwadago a Najeriya sun sanar da fara yajin aiki daga karfe 12 na daren Laraba 26 ga watan Satumba.
Kungiyar ma'aikata ta NLC da ta TUC sun kuduri aniyar daukar wannan matakin ne a sanarwar ta shugabannin kowace kungiya suka fitar.
Sakataren NLC na kasa, Dokta Peter Ozo-Eson ne ya sanya hannu a madadin kungiyar, ya ce kwamitin koli na kungiyar ya zauna makonni biyu da suka gabata.
Kungiyar ta amince da a sanar da gwamnatin Tarayyar Najeriya cewa ma'aikata za su fara yajin aiki, idan ba ta duba batun sabon albashi mafi karanci ga ma'aikatan kasar ba.
Ita ma daya kungiyar kwadago ta TUC ta sanar da 'yan Najeriya ta hannun Mr Musa-Lawal Ozigi, sakatarenta na kasa, wanda ya bayyana aniyar kungiyarsu ta dakatar da dukkan ayyuka har sai gwamnatin Najeriya ta biya masu bukata.
Sanarwar ba ta bayyana lokacin da yajin aikin zai kare ba, amma ta yi kira ga 'ya'yan kungiyar da su tabbatar da an dakatar da ayyukan gwamnati a fadin kasar.

No comments

Powered by Blogger.