Tambuwal Ya Fice Daga APC Zuwa PDP
Bayan kusan makonni ana rade-radin fitarshi daga jam’iyyar APC, a safiyar yau gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana anniyar shi ta ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa tsohuwar jam’iyyar shi wato PDP. Tambuwal ya bayyana wa dandazon magoyan bayanshi anniyar ficewar shi daga jam’iyyar ne, bayan a cewarshi ya samu shawarar yin hakan daga dubban magoya bayan shi da ma masu ruwa da tsaki a jihar. ‘Wannan ba shawara ta bace ni kadai, shawara ce ta mutane masu yawan gaske, cikinsu har da masu ruwa da tsaki a al’amuran siyasar jihar Sokoto, inda a karshe muka cimma matsayar canja sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.’ Inji Tambuwal Tambuwal yace; shawarar magoya bayan mu, da abokanmu ba abinda zamu yi watsi da shi bane, wannan shine babban dalilin zamewar mu shugabanni. Ya kara da cewa; mun fice daga APC ne zuwa PDP don mu tabbatar talakawa sun samu cimma bukatunsu na rayuwa, kamar ingantaccen kiwon lafiya, tsaro, da sauransu
No comments