Ba Ruwan Shugaba Buhari A Kan Batun Tsige Gwamnan Binuwai –Fadar Shugaban Kasa
Fadar Shugaban Kasa ta yi tir da kokarin da wasu ke yi na alakanta shugaban kasa, Muhammadu Buhari da rikita-rikitar da ke aukuwa a Majalisar dokokin Jihar Benuwe. Babban mai baiwa Shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya nisanta Shugaban kasan da hannu a cikinta. Adesina, ya bayyana sanarwar da wasu ke ta yadawa, inda suke neman alakanta shugaban kasar da badakalar da ke wakana a Jihar ta Benuwe, a matsayin cin fuska. Adesina, ya yi nuni da cewa, ana yada wannan jita-jitan ne a kan shugaban kasan, alhali shi yana can kasar Togo yana halartar taron shugabannin kasashe renon Ingila. Adesina ya ce, ta ya ma Buhari zai saka kansa cikin aikata abin da ya saba wa tsarin mulki, a inda ‘yan majalisun da ba su da rinjaye suka zauna suka ce sun tsige gwamna, wanda ba ta yanda hakan zai iya tabbata. Ya ce, “Ai wannan tamkar zuba ruwa a bayan kwarya ne. duk mai hankali ya san hakan, sai dai masu mummunan manufa ne kadai suke danganta hakan da Shugaba Buhari.
“Irin su, a wasu lokutan za ka ji suna kira da a baiwa kowa ikonsa a yi zaman tarayya na gaskiya, a wasu lokutan kuma za ka ji su suna neman shugaban kasan da ya tsoma baki a kan harkokin Jihohin. “Shugaba Buhari, a kowane lokaci yana nan kan abin da zai tsare mutuncinsa, ba zai taba jefa kansa cikin abin da zai ji kunya ba. “Duk masu ruruta wutar rikici da gangan, sannan su komo suna neman Shugaban kasan da ya zo ya bice masu ita, za su taras da shugaban kasan ne tsaye kyam wajen bin abin da tsarin mulki ya shimfida.”
No comments