5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Sanata Sulaiman Nazif Ya Bar APC Ne Saboda Muradun Talakawan Jihar Bauchi -Abdullahi Little - Arew@Blog Sanata Sulaiman Nazif Ya Bar APC Ne Saboda Muradun Talakawan Jihar Bauchi -Abdullahi Little - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Sanata Sulaiman Nazif Ya Bar APC Ne Saboda Muradun Talakawan Jihar Bauchi -Abdullahi Little

Cikin makon da ya gabata ne aka samu wasu Sanatoci da ‘yan majalisun tarayya suka koma jam’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya, cikin su akwai SANATA INJINIYA SULAIMAN NAZIF mai wakiltar Bauchi ta arewa a majalisar dattijan Nijeriya. Don jin karin haske game da dalilan da suka sa Sanatan sauya sheka wakilin mu MUAZU HARDAWA a Bauchi ya tattauna da kakakin Sanatan ALHAJI ABDULLAHI DAUDA LITTALE inda ya yi karin bayani game da dalilan da suka haifar da sauyin shekar, ga yadda hirar su ta kasance:

Leadership Hausa Newspapers SIYASASanata Sulaiman Nazif Ya Bar APC Ne Saboda Muradun Talakawan Jihar Bauchi -Abdullahi LittlePublished 47 mins ago on August 2, 2018 By Muazu Hardawa Cikin makon da ya gabata ne aka samu wasu Sanatoci da ‘yan majalisun tarayya suka koma jam’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya, cikin su akwai SANATA INJINIYA SULAIMAN NAZIF mai wakiltar Bauchi ta arewa a majalisar dattijan Nijeriya. Don jin karin haske game da dalilan da suka sa Sanatan sauya sheka wakilin mu MUAZU HARDAWA a Bauchi ya tattauna da kakakin Sanatan ALHAJI ABDULLAHI DAUDA LITTALE inda ya yi karin bayani game da dalilan da suka haifar da sauyin shekar, ga yadda hirar su ta kasance: A zamanka na kakakin Sanata sulaiman Nazif, me za ka ce game da dalilan da suka sa shi komawa jam’iyyar PDP? Suna na Alhaji Abdullahi Dauda Little, hakika ina cikin masu magana da yawun Sanata Sulaiman Nazif, don haka zan bayyana hakikanin abin da ke tafiya na gaskiya ne ya koma jam’iyyar PDP kuma shi da wasu abokan aikin sa. Saboda a zamansa na babban dan siyasa a Jihar Bauchi da kasa baki daya  ya ke jajircewa wajen kare hakkin talaka. Kuma yana yin siyasa ne don mutane su ci gaba su gane ‘yancin su da abin da zai ciyar da su gaba, don haka baya yarda da zalunci ko yaudara a siyasance, talaka ya sa a gaba don a samar da abu mai amfani da mutanen baya za su zo su ci moriya komai dadewa.

No comments

Powered by Blogger.