5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 LABARAIKotu Bayar Da Umarnin A Cafke Shugaban Hukumar INEC - Arew@Blog LABARAIKotu Bayar Da Umarnin A Cafke Shugaban Hukumar INEC - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

LABARAIKotu Bayar Da Umarnin A Cafke Shugaban Hukumar INEC

Babbar kotun birnin tarayya ranar Laraba ce ta bayar da umarnin cewa a kama, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Mahmood Yakubu saboda yadda yake kin umarnin kotiu. Mai shari’a Stephen Pam shi ne wanda ya bayar da umarnin, saboda shi Mahmood ya kashi kasancewa, a kotu a karo na uku saboda ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa. Shi dai Mai Shari’a Pam ranar 5 da kuma 10 ga watan Yuli, ya bada umarnin Mahmood ya zo kotu, ya kuma bayar dalilin da zai sa ba za a tura shi gidan yari ba, saboda rashin bin umarni. Lokacin da aka ci gaba da sauraren karar ranar Laraba Adegboyega Awomolo wanda lauya ne na Mahmood, ya bayyana wa kotu cewa, wanda ya ke wakiltar baya nan saboda ya tafi Mali wajen wani aiki da aka aike shi ya yi. Mr Pam ya ce, kotun ba za ta sa ido tana kallon mutum wanda shi Farfesa ne na  shari’a, a mayar da shi kamar wani yaron gida
Wannan ba wani abin dadai bane saboda wani babban lauya ya ki bin umarnin wannan kotun, saboda laifin da shi ya aikata. Ba za a iya ci gaba da yadda ake yi ma wannan kotun rikon sakainar kashi ba, maganar rashin bin umarni dole a dauki mataki. Shi alkalin ya ga kuskuren wasikar da Mr Awomolo ya bada mai ranar 27 ga watan Yuli, inda yake ba da dalilan da suka sa, Mahmood bai bayyana a kotu ba. Saboda ta saba ma wata wasikar da aka rubuta mai dauke da ranar 29 ga watan Yuli.

Don haka ya bada umarnin cewar a kama Mahmood saboda halayen da yake nunawa, wajen rashin bin umarnin kotu, an dage sauraren shari’ar zuwa 8 ga watan Agusta. An bada damar a kama Farfesa Yakubu Mahmood shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, wannan irin halin da yake nunawa na rashin bin umarni kotu, ba wanda zai kara yadda da aikata hakan. Tun farko dai ita kotun ta soke wata bukata da Mr Awomolo ya bukata ranar 31 ga watan Yuli, don a tsaya, kada a dauki wani mataki har sai an tsaya ma daukaka karar wadda aka yi. Alkalin ya ki amincewa da hakan saboda a cewar shi abin ya saba ma sashi na 360 na yadda ake gudanar da shari’ar aikata laifi, wadda kuma bata damar ci gaba da sauararen al’amarin daya shafi aikata laifi ba. Ana iya tunawa cewar Mr Oguebego ya yi wani abinda ke nuna aikata laifin shi, shugaban hukumar zabe , saboda yaki bin umarnin kotun koli na Disamba 2014, inda aka bukaci da ya yarda shi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP  na jihar Anambra.
Lauyan Mr Oguebego, James Odiba ya bukaci kotun  ta aika da Mahmood zuwa gudan kurkuku, saboda baya bin umarnin kotu.




No comments

Powered by Blogger.