Jarumin Kannywood Ya Karrama Ganduje
Fitaccen jarumin nan na Kannywood kuma mai shirya fina-finai da bayar da umurni, Ali Nuhu, ya karrama Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a bisa taimakon da yake baiwa masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood. A ranar Asabar ne ya mika ma shi kyautan karramawan a lokacin da yake kaddamar da daya daga cikin fina-finan na shi na baya-bayan nan mai suna, MUTUM DA ADDININ SA, a gidan gwamnatin Jihar ta Kano. An shirya fim din ne domin ya nuna wa ‘yan Nijeriya yadda za su zauna lafiya da junansu duk da bambance-bambancen Addinnai a tsakanin su, domin samar da ci gaban kasa. Masana’antar ta Kannywood, tana daya daga cikin masana’antun shirya fina-finai mafiya habaka a kasarnan baya ga ta Nollywood. Cikin sama da shekaru 25 da kafuwarta, masana’antar ta samar wa da dimbin matasa ayyukan yi a sashen arewacin kasarn
No comments