Ba Mu Da Matsalar Mai Tsaron Raga, In Ji Kocin Madrid
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Julian Lepatugui ya bayyana cewa kawo yanzu kungiyar ba ta matsalar mai tsaron raga kuma idanma kungiyar bata siyo mai tsaron raga ba basu da matsala. Real Madrid dai tana zawarcin mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thibaut Courtois wanda a kwanakin baya aka bayyana cewa ya amince da albashin da Real Madrid din zata dinga biyansa idan yakoma. Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kuma a nata bangaren ta bayyana cewa ba ta da niyyar siyar da mai tsaron ragar nata duk da cewa saura shekara daya kwantaragin mai tsaron ragar yakare a kungiyar kuma har yanzu babu wata tattaunawa akan cigaba da zaman nasa a kungiyar. Bayan wasansa na farko a kungiyar Real Madrid wanda kuma yasha kashi a hannun Manchester United a gasar share fagen fara kakar wasa mai zuwa da akeyi a kasar Amurka mai koyarwar ya ce baya damuwa da maganar mai tsaron raga. “Bana Magana akan ‘yan wasan da bana kungiya taba saboda haka ina farin ciki da masu tsaron ragar da muke dasu kawo yanzu kuma bazanyi Magana akan mai tsaron ragar da baya kungiya tab a” in ji Lepatugui. Yaci gaba da cewa “Real Madrid babbar kungiya ce kuma duk dan wasan duniya yanason ace yana bugawa Real Madrid wasa amma kuma sai dai idan munji muma muna bukatarsa saboda bazamu siyo abinda bama bukata ba” Kawo yanzu dai akwai masu tsaron raga matasa guda uku a kungiyar banda Kylor Nabas da suka hada da Luca Zidane da Kiko Casilla da kuma sabon mai tsaron ragar da kungiyar ta siya a satin daya gabata Andry Lunin. A gobe Asabar dai Real Madrid zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta Jubentus a wasan sada zumunta sai dai dan wasa Cristiano Ronaldo bazai samu damar buga wasan ba.
No comments