Zan Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Daga Ranar Da Na Shiga Ofis- Atiku
Muhammad Dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kawo karshen yajin aikin da Malaman Jami’o’i ke yi a kasarnan, inda ya ce; daga ranar farko da fara aikinsa a Ofis a matsayin shugaban kasar Nijeriya idan har aka zabe shi, zai tabbata ya kawo karshen yajin aikin Malaman Jami’o’in. Atiku ya yi wannan bayanin ne a Legas, ranar Lahadi da yamma, a cikin shirin na Silverbird Man na shekara. Ya ci gaba da cewa; yajin aikin da ake yi na daliban jami’a a kasar na tsawon lokaci kusan watanni hudu “abin kamar wulakanci” kuma wannan zai zama aikinsa na farko daga ranar da ya shiga Ofis idan aka zabe shi a matsayin shugaban Nijeriya a zaben 2019. Atiku ya ce, “Na yi matukar damuwa da cewa yayin da na ke magana, ɗalibanmu na jami’a a faɗin ƙasarnan suna zaune a gidajen su saboda yajin aikin da ake yi na ASUU.” “Idan na sami shugabancin da nake nema, aikin da zan fara na farko a ranar da na shiga Ofis, zan kawo ƙarshen wannan mummunan yajin aikin domin ‘yan makaranta su koma karatunsu.”
Tsohon mataimakin shugaban ya kara da cewa ilimin yana taka muhimmiyar rawa wajen samun nasara ga kowanne mutum ko al’umma kuma ya kara da cewa idan ya zama shugaban kasa na Nijeriya, gwamnatinsa za ta baiwa ilimi muhimmanci ta hanyar ninka kasafin bangaren ilimi a kasafin kudi na shekara-shekara da gwamnatin tarayya ke yi. Ya tabbatar da cewa; bangaren ilimi wanda ake baiwa kashi 7 cikin 100 na kasafin kudin a yau, zai tabbata da ya kai shi zuwa kashi 20 ma.
No comments