'Yan bindiga sun kashe yayar Sanata Marafa a Zamfara
Sanata Kabir Marafa |
An yi jana'izar mutum 14 da 'yan fashin daji suka kashe bayan far wa garuruwansu na Tudun Wadan Mai Jatau da kuma Ruwan Baure cikin jihar Zamfara.
Daga cikin mamatan har da Hajiya Ahadi, yaya ga dan majalisar dattijan Nijeriya Sanata Kabir Marafa, wadda 'yan fashin suka harbe kafin su yi awon gaba da mai gidanta.
Jihar Zamfara dai ta dade tana fama da matsalar tabarbarewar tsaro.
Kuma a yanzu, kasa da mako biyu kafin babban zaben kasar, mutanen kauyuka da dama na ci gaba da tsere wa muhallansu saboda karuwar hare-haren 'yan fashi.
An fara jana'izar Hajiya Sada'atu wadda ake yi wa lakabi da Ahadi ne da safiyar yau Talata a garin Wonuka cikin gundumar Ruwan baure, bayan 'yan fashin sun sa bindiga sun harbe ta a baki cikin daren jiya.
Sai kuma Tudun wadan Mai Jatau, inda aka binne gawawwakin mutum 13 da tsakar ranar yau Talata.
Baya ga mutanen da 'yan fashin suka kashe, sun kuma saci mutum biyu a garin Ruwan Baure sai kuma mutum daya a garin Kundumau da kuma Unguwar dinya, inda suka sace wata mata kamar yadda wani basaraken yankin ya shaida wa BBC.
Abubakar Abdullahi Tsafe makusanci ga sanata Kabiru Marafa ya shaida wa BBC cewa rasuwar Hajiya Sa'adatu ta dimauta dan majalisar dattijan kwarai.
Wannan hari na zuwa ne kasa da mako guda bayan kashe mutum 9 a garin Tudun wadan Mai Jatau da kuma jikkata wasu kimanin goma sha biyar, kafin su sake komawa jiya su banka wa garin wuta.
BBC dai ta tuntubi rundunar 'yan sanda ta wayar tarho don jin ta bakinsu kan harin amma ba a amsa wayar ba.
No comments