Ta Yi Yunkurin Halaka Dan Kishiyarta Da Ruwan Zafi
Sakamakon mahaifiyar yaron ba ta tare da mahaifin yaron
mai kimanin shekara hudu da watanni, yau kwana goma da yi masa kaciya sai matar ta tafasa ruwan zafi ta ce ya zo ya shiga a yi masa wanka.
Inda yaron yana taba ruwan ya ce mata akwai zafi sai ya matsa, daga kusa da ruwan nan take ta bi sa da ruwan ta watsa masa a bayansa.
Dan Allah ku duba ku gani idan da yaron nan ya shiga wannan ruwan zafin nan Allah ne kadai ya san irin illan da za ta yi masa.
Abun mamaki da na shiga duba yaron har kwalla na zubar. Kuma har na bar gidan ko sannu ba ta ce min ba. Yanzu haka matar tana nan a cikin garin Numan babu wanda ya ce mata ko uffan..
Daga Tanimu Pz Numan
No comments