5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Nasarar Da Fim Din Yaki A Soyayya Ya Samu Ta Kannywood Ce Gabadaya - Arew@Blog Nasarar Da Fim Din Yaki A Soyayya Ya Samu Ta Kannywood Ce Gabadaya - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Nasarar Da Fim Din Yaki A Soyayya Ya Samu Ta Kannywood Ce Gabadaya

Daga Mubarck Umar
Tun lokacin da aka saki film din YakiASoyayya a sinimar Film house da ke Kano, rahotanni ke ta bulla kan yadda film din ke samun karbuwa a wurin ‘yan kallo.
A zahiri, musamman idan aka yi la’akari da yadda masana’antar ke tafiya, Yaki A Soyayya ya samu gagarumar nasara. Saboda haka na yi nazari kan manyan ababen da zan iya cewa suna maqasudin nasarar film din.
LABARI:
Labarin film din ya dace daidai da matsalolin masoya a wannan zamanin, wanda a wasu lokutan suke rasa ainihin me yake faruwa da junansu.
Yadda aka tsara labarin film ya yi ma’ana matuka, duk iya bin kwakkwafin mutum, ba zai iya gano me zai faru a gaba ba, sabanin wasu finafinan da kana fara kallo, ka san kwanan zancen.
DANDALI (LOCATION)
Watau masu shirya finafinan Hausa har yanzu sun kasa gano cewar yawan amfani da location iri daya wajen shirya finafinai na rage kwarjini. Za ka film goma, amma kusan gidajen da aka yi dauke su duk daya ne. Shi kuma dan kallo kullum yana son ganin abu sabo musamman a yanayin da zai kayatar da shi.
An yi kokari matuka wajen samar da sabbin wurare yayin daukar shirin Yaki A Soyayya.
JARUMAI:
Babu abinda za a cewa jaruman film din nan sai jinjina. Sun nuna wa duniya tabbas qanana jarumai idan suka samu horaswa za su iya yin abun kirki. Akwai mamaki matuka, kan yadda film din da babu wani babban jarumi ko darakta ya shafe tarihin kowane film a sinima.
DARAKTA:
Alfazazee Muhamnad yana bada umarni a finafinai, amma bai taba samun damar da ya barje gumin basirarsa ba sai a Yaki A Soyayya. Yadda ya sarrafa jaruman wajen samar da sakon da ake da bukata ya cancanci yabo da jinjina.
TALLA (PROMOTION)
Wasu finafinan ana kashe kudi kuma a bata lokaci wurin yin su, amma wajen tallatawa sam, sai ka rasa ina lissafin furodusa ya yake. Dole film yana buqatar tallata wa a-kai a-kai, wannan shi zai bawa ‘yan kallo damar bibiyar yaushe zai fita, har ila yau, a rika jin ra’ayoyin ‘yan kallo bayan sun kalla. Hakan zai sa wadanda ba su zo ba garzayowa don su ganewa idonsu.
LOKACI:
Watau na dade ban ga film din da aka dauki tsawon lokaci ana shirya shi kamar YakiASoyayya ba. Duk da cewa jaruman da suka ja ragamar fim din su hudu ne kacal, amma hakan bai hana masu shirya fim din bata lokali wajen yin abu mai kyau.
TOKACI:-
Kamata yay masu shire fina-finai a kannywood suyi murna da nasarar da fim din yaki a soyayya ya somu, domin an nuna yadda masana’antar ka aya yin abin kirki ba tare da la’akari da baboon darakta, jarumi, marubuci, ko kamfani ba.

No comments

Powered by Blogger.