Me Buhari Ya Je Yi Kano?
A ranar Alhamis ne jirgin yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari ya sauko a Kanon Dabo.
BBC ta tattaro maku wasu daga cikin abubuwan da zai aiwatar yayin ziyarar.
Baya ga kamfe, bayanai sun nuna cewa shugaban kasar ya zabi ya kaddamar da wasu ayyuka guda biyu daga cikin shida da aka gabatar masa wadanda gwamnatin jihar ta aiwatar.
Ayyukan su ne bude hanyar kasa ta Kofar Ruwa da ke kan titin Katsina, sai kuma gadar sama ta kan titin Murtala Muhammad, dukansu a kwaryar birnin Kano.
Ana kuma sa-ran shugaban zai kai ziyara fadar sarkin Kano domin gana wa da Sarki Muhammadu Sanusi II.
Sai dai zuwan Buhari Kano don yakin neman zabe, ya zo da takaddama a tsakanin ‘yan siyasa da sauran al’umma a ciki da wajen jihar, musamman bisa la’akari da hotunan bidiyon, da ake zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da karbar rashawa.
Duk da dumbin muhimmancin wannan ziyara ga shugaban kasar da ma gwamnan jihar na nuna wa abokan adawa karfin farin jinin da suke da shi a jihar wadda ta kasance mai yawan jama’a a kasar, takaddama da ce-ce-ku-ce, sun zamewa zuwan shugaban kasar wani tarnaki.
Magoya bayan gwamnan jihar, na fatan cewa wannan ziyara ta shugaba Buhari, za ta kawo karshen rade-radin tsamin dangantakar da ake zargi ta shiga tsakanin Ganduje da Buhari.
Magoya bayan gwamnan jihar, na fatan cewa wannan ziyara ta shugaba Buhari, za ta kawo karshen rade-radin tsamin dangantakar da ake zargi ta shiga tsakanin Ganduje da Buhari.
Wasu dai na cewa wai shugaban kasar a yanzu, baya ma son hada hanya da gwamnan na Kano, ballantanama har ya sake daga hannunsa ya ci zabe.
Wannan dambarwa dai ta taso ne watanni hudu da suka shude a lokacin da aka fara kwaza labarin cewa an dauki hotunan gwamnan na Kano na karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila, kafin daga bisani jaridar Daily Nigerian ta fitar da wasu hotunan bidiyon da suka nannaga wannan zargi.
Gwamnatin jihar Kano dai ta musanta wannan zargi, inda daga bisani ma ta shigar da dan jaridar da ya wallafa bidiyon a kotu.
Duk da wannan dambarwa, akwai dumbin magoya bayan shugaban kasar da suke maraba da zuwansa, wasun su ma domin su ji inda gwamnatinsa ta kwana game da wannan zargi da ake yi wa gwamnan na jihar Kano.
Wani daga cikin magoya bayan shugaban kasar ya shaida wa BBC cewa’ Talakawa sun zuba ido su gani ko mai girma shugaban kasa idan ya zo jihar Kanon, zai daga hannun gwamna Ganduje ko kuma akasin haka’.
Wannan batu na karbar goro da ake zargin gwamnan na Kano, shi kowa ke jira ya ji matsayin shugaban kasar a kai.
A bangaren ‘yan adawa a jihar kuwa, cewa suka yi su sam ba sa maraba da wannan ziyara ta shugaban kasar.
‘Yan adawan sun shaida wa BBC cewa, su fa ba sa farin ciki da wannan ziyara domin kuwa ba bu abin da shugaba Buharin ya yi wa jihar Kano sai gidan ‘Kurkuku’.
No comments