Majalisar Dokokin Lagos Na Yunkurin Tsige Gwamna
Ga dukkan alamu yunkurin da ‘yan majalisar dokoki a jihar Legas ke yi domin tsige gwamnan jihar na neman dagula siyasar jihar.
Hakan na faruwa ne bayan da ‘yan majalisar dokokin jihar, suka kira wani taron gaggawa a kan gwamnan jihar Mista Akinwumi Ambode, kan ya gurfana don kare kansa a gabansu cikin mako guda.
Ana zargin Mista Akinwunmi da gaza gabatar da wani bangare na kasafin kudin jihar na shekara ta 2019 da ake zargin ya yi babakeren aiwatar da kudin kasafin ba tare da amincewar majalisar ba.
Tuni dai wasu magoya bayan gwamnan suka fito zanga-zangar nuna adawarsu da yunkurin dakatar da gwamnan, da kuma bayyana yadda kiri-kiri aka hana gwamnan tikitin takara.
Ana dai ganin ba a yi wa gwamnan adalci ba, ganin cewa duk da matsin da ya ke fuskanta daga jam’iyyar APC, hakan bai sa ya dai na mata biyayya ba.
Babban mai tsawatarwa a majalisar dokokin jihar Honourable Akume Ade, ya ce za su yi wa kowanne bangare adalci kan bukatun da suka gabatar.
Ya ce ”ba wane hargitse a jihar mu, kuma ba za mu bari wannan lamari ya illata harkokin ci gaban gwamnati ba, kuma abin da ke faruwa yanzu ba wane abu ba ne face duba yadda gwamnati mai ci ta tafiyar da kasafin kudi kamar yadda doka ta shata.”
Kwanaki biyu kenan a jere da ‘yan majalisar Legas ke taron gaggawa a kan zargin da suke yi wa gwamnan da gaza aiwatar da kasafin shekara ta 2019 da kusan kashi 50 cikin 100.
‘Yan majalisar sun bai wa Gwamnan mako guda ya bayyana a gabansu domin kare kansa daga wadanan zarge-zarge na fitar da kudi ba tare da amincewar majalisa ba.
Mista Akinwumi, kusan ana iya cewa ya soma samun kansa cikin tsaka mai-wuya ne tun bayan da uban jam’iyyar APC a Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar ta Legas Bola Ahmed Tinubu, ya juya baya ga gwamnan.
Wannan dalili ne ya sa aka maye gurbin Mista Akinwumi da Baba Jide Sanwo-Olu, ya zama dan takarar APC a Legas.
Masu sharhi dai na ganin cewa akwai yi wuwar gwamna Akinmumi Ambode, ya rama abin da jam’iyyarsa ta yi masa a zabukan kasar da ke tafe.
No comments