5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Najeriya Ta Sayi Sabbin Jiragen Yaki 18 Don Yakar Boko Haram - Arew@Blog Najeriya Ta Sayi Sabbin Jiragen Yaki 18 Don Yakar Boko Haram - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Najeriya Ta Sayi Sabbin Jiragen Yaki 18 Don Yakar Boko Haram

Nigerian army
Rundunar sojin sama ta Najeriya na jiran isowar wasu sabbin jiragen yaki guda 18 domin yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashi.
Babban hafsan sojin sama na kasar Air Marshal Sadique Abubakar ya ce suna jiran isowar jiragen yaki shida masu saukar angulu daga Italiya da kuma wasu jiragen soji guda 12 daga Amurka

Jaridun kasar sun ambato shi yana tabbatar da haka a yayin bude wani sabon dakin tiyata na zamani a asibitin sojin sama da ke Kano.
Ya ce jiragen za su taimaka wajen murkushe Boko Haram a arewa maso gabashi da kuma masu satar mutane a sassan arewacin kasar.

Tuni ma’aikatar tsaron Amurka ta sanar da ba da kwangilar kera wa Najeriya jiragen yaki guda 12 samfurin A-29 Super Tucano.
Tun a watan Afrilu ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da odar jirajen bayan doguwar tattaunawa da gwamnatin Amurka, matakin da ya kai ga sassauta dakatar da sayar wa Najeriya da makamai.
Ana sa ran kammala aikin kera sabbin jiragen zuwa 2024.
Gwamnatin Najeriya ta ce jiragen za su taimaka wajen karfafa tsaro a kasar da kawo karshen yaki da Boko Haram.
#BBCHAUSA

No comments

Powered by Blogger.