5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 KHAIREEYYAH Hausa novel part 1 - Arew@Blog KHAIREEYYAH Hausa novel part 1 - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

KHAIREEYYAH Hausa novel part 1



PART 1
 *{ ```Page 1~5```}*

          Tafiya take a buge akan titi kamar zata fad'i kasa, ga kwal6an(bottle) hernesy a hannun ta na dama, bottle na champagne a hannun ta na hagu, idan ta kurba Hernesy ta kurba champagne(giya/wine),da dare misalin karfe sha d'ayan dare a garin maiduguri, ko ina tsit sai motoci d'addaya da suke wucewa da yake garin ba kamar da ba kowa na shiga gida da wuri sabida condition na garin,wani mota neh ya zo da gudu yana mata horn amma inaa hankalin ta baya jikinta ta, kwasss motar ya kwashe ta tafad'i a kasa... 
        _Few years back_
(```shekarun baya```)
             "Imrann, Imrann" wata yarinya ce wacce bazata wuce shekaru goma sha bakwai (17yrs) ba ita take ihun kiran sunan Imrann(tsaban ihun ta ni kaina sanda na firgita, ni nana kallo nabita dashi baki  bud'e)
     
              Uniform na makaranta neh ajikin ta, riga fari da wani dan mini skirt light brown wanda bai kai gwiwa ba ahaka kuma wai sch uniform, wani shegiyar high heel neh a kafar ta bak'i da white socks d'inshi. Gashin kanta nan abude ta kama da ribons pink da blue had'addu, ta sha make up kamar ba makaranta zata ba,  wayan ta tacire acikin jakar ta kirar Samsung Galaxy S7 ta daga sama ta tura baki(Eesha ta cemi selphie zata dauka)bayan ta gama d'aukar hoto ta maida wayar a wani tsadadden jakar ta pink colour, sai waige waige take, wani ta hango yana wanke mota a gefe, wani dogon tsoki taja tace
         Kai Garba (wani tsoho takira wanda a haifa yayi jika da ita) wai ina shegen driver nah Imraan neh baisan nayi latti din makaranta ba'
    Tsohon nan wanda takira sa da Garba yace ''hajiya wlhy da kyar mukayi bacci jiya baya jin dadin jikinsa neh d'an nawa'"
     Kallon uku saura kwabo ta watsa masa kan taja tsoki tace
     " Garba da kai da yaron ka kullum sai kawo excuses mtsewwww, idan baza ku iya aikin ba basai mu nema wasu ba, ai duk Abba neh yake raga muku da zai bi shawara ta da tuni nayi outttt daku, Nonsense".. 
              Codein tazuba acikin coke tafara shaa tana had'awa da Roci agaban Garban ba kunya (nayi salati nagode wa Allah, yara kanana da shayeshaye duniya ta 6aci Allah ka bamu yaya nagari)

         Shiga mota tayi ta tada ta danna horn da karfi mei gadi ya bud'e mata gate, fisgan motar tayi ta bar haraban dankareran gidan su, gudu take sharawa akan titi kamar na uban ta har takai wani Babban makaranta da aka rubuta CARE BAZE PRIVATE SCH,  tashiga tayi parking d'in motar ta, tafita a motar tana taku kamar hawainiya da hankali, ta wuce class direct 

        Tana shiga class aka fara ihun  "rude gurl, rude gurl" koh kulasu batayi ba ta zauna a seat dinta, ta cire wayar ta ajakar ta tayi posting hoton d'azu da ta d'auka a Instagram da Snap chat nan da nan tasamu kusan 2K likes, tana chating tana shan coke dinta.. 
           Ba'afi minti biyu ba malamin physics yashigo, aji yayi tsit kowa ya kama kansa, ya fara lecture yaji kas kas karan cingam (chewing gum), juyawa yayi yana kallon su d'aya bayan d'aya yace
   "Who the hell is chewing gum in my class"
   Daidai nan ta kara kakas da chewgum nata, kallo ya watsa mata ranshi yayi bala'in 6aciwa daman ya ki jinin yarinyan dan bata da tarbiya koh kad'an yace
 " *Khairiya* getout of my class"
       Cigaba da cin cingum nata tayi kamar bata ji shiba
      Tsawa ya kara daka mata yace "I said get outtt of my class you Moron"
        Tashiwa tayi ta d'auka roban coke nata wanda ta had'a da codein, ta d'au wayar ta, zuwa tayi dab kusa dashi, ta kallesa sama da kasa tace
     "U can send me out of your damn class but let me warn you, don't u ever i mean e--v-e-r call me a Moron u filthy fool"
 Taja wani dogon tsoki ta fice a ajin, ajin ya d'au ihu ana cewa rude gurl rude gurl  (wa'iya zubillah)
       Shiga motar ta tayi ta kuna ra6a (AC) tana jin music na lilwayne I feel like dying tana shan coke d'inta....

       Can bayan malamin physics ya fita ta dawo ajin ta zauna, bata kara tashiwa a ajin ba sanda aka tashi a makarantar, fisgan motar ta tayi ta wuce wata had'addiyar shopping mall
        Tana shiga tana cin cingum kamar irin tsofin yan bariki, ga codein yana aiki tana tafiya kamar zata fad'i ga wani baccin dayake fisgan ta (slow inji masu sha), bata san lokacin da ta buge wata tsohuwar mata ba duk suka fad'i har kasa..
     Khairiya tana tashiwa tace ke wace irin bahuwar tsohuwa ce, baki kallo neh ehh tsohuwa, ta fad'a da tsawa
     Mari taji mei rai da lafia akan kyakkyawan fuskar ta, aka kara mata wani marin, sanda aka wanke ta da mari lafiyayyu guda uku masu kyau yace
    "Ke wace irin dabba ce, kinsha kwaya kin bugu shineh zaki bangaje mutum kuma kizo kina zagi"
    Bud'e ido tayi ta kallesa mei kyau, ta nema baccin ma ta rasa, kallo ta bishi dashi tace
    "Who the hell are you da zaka ta6a lafiya ta, kasan ni yar wacece, Sunana *Khairiya Ibrahim Muhammad*, yarinyan *Alhaji Ibrahim Muhammad Fu'ad mai Naira*, ka ta6o bala'i da masifa, sai kayi regretting mari nah da kayi, wlhy koh kai d'an gidan waye neh"
   Cire wayar ta tayi ta danna kira, ana picking tace " ina Nedd Grocery kuzo nan da minti biyu" ta katse wayan
     Tsohuwar matar nan sai cewa take wa yaron da suke tare " *Zil* mu wuce ni na hakura tunda ka mare ta ai shikenan ka rama mini muje gida pls dan Allah "
    Wanda tsohuwar takira da Zil yace "Haba Hajja kibari na koya mata hankali, yarinya ba tarbiya asaran haihuwa, tirrr wlhy na tausayawa iyayen ki"
    "Kai neh iyayen ka sukayi asarar haihuwar ka bani ba, *You filthy wretch*" tofa masa miyau bakin ta tayi sai farar shaddan sa
     Bai san lokacin da ya jata waje ba suka bar mall d'in, yafara jibgan ta, duk kokarin ta dan ta rama amma inaa karfin su ba d'aya ba, mutaneh suka zo raba wa amma yaki barinta, ana cikin haka motoci guda uku suka tsaya, manya manyan karti neh, idon su ja bakin su bak'i, da wuk'a da adda suka fito wanda ya nuna tabbacin 'yan daba neh
    Suna fita a cikin motar su suka hau kan saurayin wanda aka kira da *Zil* suka fara jibgan sa, sanda suka masa likis da duka jiki duk jini, kiran police akayi suna ganin police  suka hanzarta saka Khairiya a mota suka gudu

 *```{Page  6~8}```*
         Har kofan gida suka kaita, bud'e zip na jakar ta tayi ta cire bundle na d'ari biyar ta mika musu, sai godiya suke mata suka hau motar su suka tafi, horn tayi da karfe aka bud'e mata gate tashiga, da kyar ta iya takawa zuwa falo tana d'ingishi dan tasha duka
      Tana shiga parlour ta baje akan kujera, masu aiki neh har uku suka zo kanta suna gaishe ta hajia Ina yini
     Koh amsawa batayi ba tace
   "Haule kije ki kawo ruwan zafi da towel" toh hajiya wanda aka kira da haule tabar wajen
    Khairiya ta kara juyawa tace "Indo kunna mini TV ki mika mini remote" hakan kuwa Indo tayi
   Sai ta kara juyawa wajen d'ayan mai aikin tace "Dije wani abinci kika dafa"
   Dije tace abinda kikace na dafa da safe hajiya
    Wani kallo khairiya ta watsa mata tace "da ban manta ba zan 6ata lokaci nah na tambaye ki neh very stupid mata kawai"
    Dije ta durkusa har kasa tana cewa hajiya kiyi hakuri sauce na kwai da coconut rice na dafa
    Wani dogon tsoki Khairiya taja sannan tace "toh yanxu banso na cishi, soya mini plantain sai ki had'a mini da pizza nah ki kawo mini"
    Dije ta durkusa har kasa tace toh hajiya, Haule tazo da abun da Khairiya tace ta kawo ruwan zafi da towel
    Khairiya ta tashi ta shiga d'akinta tacire uniform na makarantan ta tad'aura towel ta fito zuwa parlour, tacewa Haule
   "Zoki matsa mini jiki"
Haule ta tsuguna tafara matsa mata da ruwan zafin, tagama ta shafa mata aboniki (man zafi), hajiya mei yasamei ki haka
    Kallo Khairiya ta watsa mata tace "Ina ruwan ki dani, nifa bana son gulma, iyayen da suka haife ni ba mance wa dani sukayi ba, ke ina ruwan ki"
    Haule sai hakuri take bata tana cewa hajiya kiyi hakuri dan Allah, tsoki khairiya taje tace "oya tashi ki bani wuri" Haule ta tashi tabar mata parlour
      Kallon TV take a channel na Dubai sport suna nuna games da akeyi na Olympic Rio wanda akeyi a Brazil, wayan ta neh yafara ringing, screen d'in ta kura wa ido, number neh yake kiran ta amma ba code na nigeria baneh, tasan Abba baya Nigeria yana Qatar amma wannan ba code na Qatar baneh, d'aukan wayan tayi tasaka a loudspeeker ta ajiye a table na gaban ta tace
   "Hello"
Dagacan 6angaren muryan wata mata neh mei zak'in gaske tace
    "Baby nah yakike, ina ta trying number ki for the past sati biyu amma baya shiga"
      Khairiya ta numfasa, tayi shuru na wasu second (dakikai) batace komai ba, matar takara cewa
   "Daughter na bakya ji neh koh network naku bakyau"
    Khairiya katse wayan tayi taja wani dogon tsoki, haka wayan yana ringing bata d'auka ba sai can daga baya ta d'aga wayan,ta saka a loudspeaker ta ajiye a cinyan ta, matar tace
    "Hlo haba baby nah kiyi hakuri zanzo na duba ki very soon, your mum really miss you karki damu zanzo kinji baby"
    Tun Khairiya na hawaye har ta fashe da kuka, matar nan tana jin kukan Khairiya tace
   "No pls don't cry baby nah, kiyi hakuri kinsan halin Alhaji bature baya bari nah sosai amma will have time nazo na duba ki I promise you, na miki alkawari kinji pls kidai na kuka, yanxu Ina Brazil kinsan ana Olympic games a wajen, Ina Abban ki"
     Khairiya tana kuka tace "Ammi yanxu har mijin ki yafi miki akan 'yarki na cikin ki, sai kiyi sati biyu, uku wata d'aya ba tare da kin kirani ba, kiyi shekara bakizo dubani ba, dan Allah kar ki sake kirana ma na hakura" ta katse wayar
    Wani kuka ta fashe dashi, sanda tayi mai isarta tayi shuru, kwalawa Haule kira tayi, Haule tazo ta durkusa a gabanta tace hajiya gani
  Khairiya tace "Haule yau wace rana"
Haule tace "Hajiya yau Alhamis"
      Khairiya tace "ke ni bansan miki wani Alhamis ba idan zaki mini da yaren da zan ganeh toh "
   Haule ta durkusa tace "Hajia kiyi hakuri yau Thursday"
    Mtsew shineh sai kin 6ata wa mutum lokaci, shiga ciki ki d'aukan mini hijabi nah da Qur'ani nah yau malamin nan zaizo nayi sallah na koya hadda, kuma kicewa Dije idan bata kawo abincin nan a minti d'aya ba toh abakin aikin ta, very lazy people kawai 

       Can da daddare bayan Sallah isha'i malam Ali yazo, shineh malamin da yake kara mata Qur'an, tun da tazo duniya bata ta6a ganin mutumin da take shakkan sa kamar Mallam Ali ba, ita kanta abun mamaki yake bata, idan yakara mata karatu zama take tsakanin ta da Allah dan ganin ta haddace, bayan yazo ta basa hadda yamata karen karatu ya tafi, tana shiga d'akin ta taga wayan ta yana ringing, Swt Abba a rubuce akan screen d'in, da sauri ta d'auka tana murmushi tace
    "My swt Abba, yaushe zaka dawo ina missing naka" tana fad'a tana tura bakin ta
   Yace kar ki damu Mamata very soon zanzo, gobe zanbar Qatar zanje Cuba akwai wani meeting da nake dashi a wajen
    Khairiya tace "gaskia Abba nagaji da zama ni kad'ai kayi aure kuma kaki"
    "Kar ki damu Mamata ina zuwa sai ki nemo mini matan aure kinji" Toh daddy tana dariya
   Abban yakara cewa "Mamata yaushe zaku fara Exams"
   "Abba zamuyi jamb Next 2weeks (sati biyu), Waec da Neco ma zamu fara wata mei zuwa
   Abba yace "Yawwa Mamata kiyi karatu kinji, hope dai Mallam Ali yana zuwa"
   "Eh yana zuwa Abba"
 "Yawwa Mamata kiyi karatu kinji, zuwa sati uku zan dawo, take care"

    Khairiya tace " ok dad" ta katse wayan, d'aukan Qur'ani tayi dan koya haddan da Mallam Ali yamata d'azu, ita a rayuwar ta bata ta6a zuwa islamiya ba, bata san komai ba sai Qur'an da Tajwid, bata san komai akan su Fiqh da Hadisai ba da sauran littatafai (yan uwa kar muce Qur'ani ya ishemu yana da kyau musan sauran littattafai is very important)
     Bayan nan tahau gadonta ta karanta fatiha, iklas, falaq, nas, da ayatul kursiyu tashafa ajikinta takwanta bacci, wayan ta neh yafara ringing, yatayar da ita daga baccin tana dubawa  taga number da d'azu Ammi takira ta dashi ne kin d'agawa tayi tacigaba da baccinta. 

*```{Page 9~10}```*
     Da asuba ta tashi tayi sallah, ta d'au Qur'ani ta biya karatun jiya, bayan ta gama ta tashi taje fridge ta d'auka totolin ta shanye tas ta d'auka Roci ta tsosa, akasa ta zube tafara bacci kamar ba gobe sai kusan karfe takwas Haule tazo ta tashe ta
   "Hajiya ki tashi ki shirya zakiyi lattin makaranta"
    Khairiya tace cikin bacci "yanxu karfe nawa neh"
  "Takwas hajiya, umm yi hakuri eight O'clock (8:00)
    Khairiya batasan lokacin da ta tashi ba, cire kayan ta tafara agaban Haule, tace
  "Haule cire mini uniform nawa, ki saka mini burger biyo da coke biyu a mota, socks nawa da takalmi na duk ki cire ki ajiye mini"
    Tana fad'a ta shiga toilet tayi wanka cikin minti biyar tafito, mai ta shafa ta saka uniform nata, zama tayi tana shafa powder (huda) Haule kuma tana saka mata socks da takalmi a kafarta, bayan tagama tace Haule fito mini da jakata mota, takwas da rabi ta shiga mota ta zauna a ownest corner, d'aukan burger tayi tafara ci tana jiran driver yaja ta har tayi minti d'aya bataga driver ba
     Fita tayi a motar tana ihun kiran Imran, amma shuru, dattijon nanne Garba yace
  "Hajiya sai hakuri wlhy baiji sauki baneh shiyasa yau ma baizo ba"
    Khairiya ta juya ta harare shi taja wani dogon tsoki tace
   "Toh abakin aikin sa, kar na kara ganin sa a gida nah, nonsense" Garba na rokonta amma ku tsaya sauraran sa batayi ba
    Shiga motar ta tayi ta fisga, kamar kullum tana gudu akan titi dan ita sam bata iya driving mota a hankali ba cikin minti takwas ta isa makaranta, karfe takwas maigadi yake rufe gate amma ita tana zuwa zai bud'e mata a kowani lokaci dan yasan halinta bata da mutunci kuma tana basa kud'i sosai
         Shigan ta class malamin Biology neh a ciki, Corper neh (d'an bautan kasa)daga Imo state, sunan sa Christopher amma ana kiran sa da Corper Chris 
        Shiga tayi ba koh excuse,taku takeyi kamar batason taka kasa, kallo ya bita dashi sama da kasa yana had'e miyau, ya dakatar da ita yace
  "Hea you, why do you come late"
     Tana tafiya tace masa
   "Issues"
  Kallon mamaki yamata yace " what's your name" yana tambayar sunan ta
     Sanda ta zauna akan kujeran ta tabaje kan tace
   *" Kim"*
     Yace "what type of name is this"
     Batare da ta kalle shi ba tace "Meaning Khairiya Ibrahim Muhammad, my friends call me Kim that's in  shortcut"
      Yana lashe le6a yace "Kim Met me after class"
   Ko ansa masa batayi ba, yana koyarwa tana d'an joter wa, dan Jamb saura sati biyu, bayan an tashi a makaranta aka basu hutu sai bayan Jamb su dawo, zata shiga motar ta kenan sai ga Corper Chris yace
   "What happen i've been waiting for you in my office"
 _(ya baki zo office nawa ba ina ta jiranki)_
    Khairiya kallon kama raina ni ta masa tace
 "Nincompoop kawai"she mumbled, ta fad'a a hankali kan tasake cewa
  "ni zanje na sameka a office, Allah sawwaka, just tell me your problem now banda time da zan samei ka a office"
    Ba abun da yaji sai just tell me your problem, abun bai masa dad'i ba amma she's too hot to ignore bazai iya barin taba, yana murmushi yace
   "Amm I just wanna say you are Hot"
    Tsoki taja ta kallesa sama da kasa tace
   "I know m HOT, u don't have to say it"
     Corper Chris yana lashe baki yace
  "Emm I want you to come to my house, so that we can catch some Fun"
     Sarai tasan mei yake nufi, tufar da miyau tayi ta kalle sa, kallon tsana tace
     "Kai amma Allah ya'isa tsakani na da kai, ni mazan larabawa da Indiya wa ma basa burgeni  balle kai inyamuri, kama cuce ni ka raina ni wlhy, bari zan koya maka hankali" ta fad'a tana murmushi
   Duk abun da take fad'a bai jiba, amma yasan bata amince ba, yace "I dnt get you Kim what do you mean"
_(Ban fahimce kiba Kim)_
    Murmushi Khairiya tayi tace
  "Dont worry Chris, just give me your address, tomorrow is Saturday right?, Expect me in d Morning around nine, I'm gonna spend the whole day with u, I love catching Fun, catching Fun is my favorite"
    Wani shu'umin murmushi yayi, mika masa takarda da biro khairiya tayi tace "write it down, I mean your address"
   Kar6a yayi ya rubuta mata har number wayan shi, yace
   "What do u want me to keep for you"
   Tayi murmushin mugunta tace
    "You, I just want you en nothing else"
    Wani dad'i yaji kamar ya kashe shi, sai godiya yake mata, ta hau motar ta ta fisge shi, tana barin haraban Makarantan Wayar ta ta kunna ta latsa numban  Kamalu bad (shineh da yaransa suka ma Zil duka a shopping mall), Kamalu badd sunan da ake kiran shi kenan, shineh babban su a 'yan ta'adda
   
      Kamalu badd na d'aukan wayan Khairiya tace
     "Akwai aiki tomorrow in the morning, kazo around nine kaji, kar kaje kana mini shirme kace baka ganeh time ba, what I mean is kazo kafin Tara na safe" koh jiran ansa batayi ba tayi hanging call d'in

*```Page 11~13```*
       Tana shiga gida tayi parking na motar ta a parking space, tafita a motan ta taji murya ta bayan ta ana cewa
    "Queen Khairiyya daughter'n Abba ya makaranta" wani dattijo neh dogo bak'i kyakkyawa yana murmushi
   Tura baki Khairiyya tafara tace
    "Ni ba ruwana da kai ai Uncle Hisham, tun da katafi Lagos sau d'aya ka kirani, ka manta dani gaba d'aya"
    Wanda takira da Uncle Hisham yace
 "Haba khair kinsan aikin mu ba Hutu, kuma ke kullum kin cika canje canjen number"
    Tayi murmushi tasan yana da gaskia dan a wata sai ta canza Sim card sau biyu wani sa'in sau uku ma, tace
   "Toh naji Uncle, yanxu ina tsaraba ta"
   "Haba khair baza mu shiga ciki mu zauna ba kina maganar tsaraba"
    Tana kumbure kumbure tace "toh mushiga"
      Suna shiga parlour Uncle Hisham ya zauna ita kuma tashiga kawo masa kayan motsa baki, gaban shi dam ta ciki dasu snacks da drinks, ba abun da yasha sai Malt, ya d'an sha kad'an yace
    "Khair Sarauniya, nazo na d'auke ki muje gida nah kiyi koh wata d'aya"
     Khairiyya tana washe baki tace
   "Laa Uncle Yaa Ammar yadawo neh"
    "A'a bai dawo ba Khairiyya sai nan da wata shida"
    Ta tura baki tace "gaskia Uncle Hisham Abba ma yace na zauna a gida baya so ana barin gidan ba kowa empty" a zuciyarta sai cewa take Tab naje gidan ka Matar ka ta hanani sakat ana zaune kalau, da Yaa Ammar yana nan neh ma toh zan iya zama amma shima bayanan ga gobe akwai catching Fun na bika Kut ai bazai yuba
      Uncle Hisham yace "Haba Khairiyya yanxu kina jin dad'in zama Ke d'aya daga ke sai masu aiki, kina yarinya karama wannan wace irin rayuwa ce ehh"
      Hawaye tafara tace "Uncle Hisham tun ina karama nake living like this miserably, ina garin da kake aiki can mahaifiya ta take, wannan maganar kuma ba ni yakamata ka mini ba Ammi ce yakamata ka mata, ita tabar loneliness helpless child"
    Shiga d'akin ta tayi da gudu ta kulle kofa tana kuka sosai, wani irin iyaye Allah ya had'a ta dasu, gwara Abban ta tasan dalilin neman da yakeyi,and she cant stop him amma Ammi fa, taje tana jin dad'in rayuwar ta ta manta dani"
     Tun Uncle Hisham na buga kofa har yagaji ya bar gidan, tana jin motar shi yabar gidan tayi sallah Zuhur tayi Asr, abinci ma ta kasa ci, tun da nazo duniya da 'yan aiki nake rayuwa, wannan wace irin rayuwa ce wai take fad'a da ihu
     Kofan d'akin ta ake bugawa, Khairiyya tace
   "Who the hell is knocking my door"
    Dije ce a kofan tace
   "Hajiya abincin ki na kawo miki"
    Khairiyya ranta ya kara 6aciwa dan idan ta shiga cikin damuwa batason kowa ya mata magana, tace
   "Dan kaniyar ki yar shishshigi ni nace ki kawo mini abinci, toh kije bazan ciba"
   "Haba Hajiya dan Allah"
  Wlhy idan na fito ranki zai 6aci kibar mini kofa nace, ta fad'a a tsawace, hakan yasa Dije ta bar wajen
       Khairiyya bud'e fridge nata tayi tasha codein da benelyn kwal6a biyu kan taji daidai, zubewa tayi a kan babban gadon ta wanda zai iya d'aukan mutaneh biyar tafara bacci, itace bata farka ba sai karfe bakwai daidai ana kiran sallar Magrib, da kyar ta iya yin sallah tsaban yunwan da takeji, rabuwar ta da saka abu a baki tun burger na safe
      Dining taje taga empty, Haule ce kawai take kwana
 a gidan, kiran Haule tayi da muryan da Allah ya bata da karfi, Haule tazo ta durkusa tace
    "Na'am hajiya ganinan"
    "Wai uban mei kikeyi a ciki inata kiranki sai yanxu kikaga daman fitowa" cewar Khairiyya
    "Hajia Wlhy kina soma kirana koh second ban karaba na fito"
   "Ahh toh sharri na miki koh, Haule ki amsa mini na d'aura miki sharri kike nufi koh"
   Haule ta sunkuyar da kai tace "Hajiya kiyi hakuri ba hakan nake nufi ba dan Allah"
      Tsoki Khairiyya taja tace "Mei Dije ta girka"
    "Hajiya Shinkafa da wake da miyan ja"
        Wani kallo Khairiyya ta watsa mata wanda yasa har cikin Haule yayi kuka kuuu, Haule muryan ta na rawa tace
   "Yi hakuri Hajiya Rice/Beans with stew"
      Khairiyya tayi jimm, ta fusgar da iska tace
   "Amma lalle Dije ta raina ni, sau nawa zan gaya mata bana son kayan tusa, musamman da daddare, cikin mutum ya 6aci inje inata tusa ina shigan toilet ba gaira ba dalili, mtseww kuma Wlhy yunwa nakeji"
     Haule tace "Hajiya koh zan dafa miki wani abincin neh"
    "Ai toh Haule da kin iya dafa abinci bazan tsaya ina 6ata lokaci nah ina miki dogon zance ba, your food makes me puke, kawai had'a mini G&G ki kawo mini banson stew"
     Haule a zuciyarta cewa take ai gwara ni ina kokarin abincin kefa, tsawan da Khairiyya ta mata shi yadawo da ita da maganan zucin da takeyi
   "Tunanin Uban mei kikeyi neh Haule, idan tunanin saurayi neh toh Allah sawwaka nidai kije ki had'o mini abinci" Khairiya ta fad'a a tsawace
    "Umm Hajia yi hakuri naji kamar kince G&G ni kuma bansan abincin ba balle na girka" cewar Haule
     Kai kai Yaa Salaam, wai ni Abba da wani irin villagers masu aiki ya had'a ni dasu neh, toh abincin kauyen ku wanda kukeci kullum, abun da nake nufi Shinkafa da wake yi mini had'in garau garau dashi yi sauri inajin yunwa"
     Haule ta tashi tayi hanyan kicin sai cewa take Allah shirya Khairiya garau garau ma baza ta iya fad'a ba sai G&G taja tsoki
      Bayan Haule ta had'a mata garau garau nata taci tayi nak, tayi alwala tayi sallan Isha'i, wayan ta ta d'auka ta kira Abba,
  "Abba yau throughout baka kirani ba fa" ta fad'a tana tura karamin bakin ta
   Abban yace "wollah Mamata i've been trying your line d'azu but baya shiga, yakike ya shirye shiryen Exams"
    Tace "Abba gaskia karatu da wahala kuma jamb wani sa'in ba karatun ka baneh a had'e da sa'a kayi wani abu dan ni inason next section nashiga jami'a"
    Abba yace "Khairiyya kiyi karatu kinji, In Shaa Allah zaki ci, now kiyi bacci you need to rest"
   "Ohk Abba sai da safe gudnyt" ta katse wayan
   Mallam Ali baizo yau ba,dan haka  shiga su Snapchat da Instagram tayi, bayan tayi dube duben ta, tayi addu'a ta kwanta bacci
     Washegari da safe bayan tayi sallan Asuba ta kwanta bacci ita bata farka ba sanda wayan ta ya damei ta da ringing, d'aukan wayan tayi batare da duba wanda ya kira ba, taji ana cewa
   "KIM muna kofan gate na gidan kifa tun d'azu ina kiranki bakya picking"
    Cikin muryan bacci "tace Kamalu badd yanxu karfe nawa"
    Yace "Kim yanxu Tara da rabi fa"
   A take ta tashi tace "Toh ka bani 30mins zan fito kaji"
    Yace ba damuwa KIM koh nan da awa d'aya neh mu masu jiranki neh
 A gaggauce ta fad'a toilet tayi wanka, dining taje taci abinci dan sauri ma bata tsaya cin mutuncin Dije ba yau ba, bayan ta gama ci ta shiga d'akinta ta saka wani dogon rigar yar kanti armless (ba hannu)mei kala red da black, ta saka jacket baki akai tayi rolling da gyale red, simple makeup tayi yau daga powder sai lipgloose da mascara,da wani Red takalmi mei uban tsayi, d'aukan paper da Corper Chris ya bata tayi ta fita parking space ta shiga motarta taja wajen gidan, a waje bakin gate nata ta gansu Kamalu badd suna zaune acikin motar su Odesys, Kamalu badd yana ganin ta ya fita a motar, yazo dab kusa da motar ta ita kuma ta sauke Glass, yace
  "KIM wani aiki neh haka"
   Khairiyya tace "wani neh nakeso mu d'an koya masa hankali"
   Kamalu badd yace "Hajiya KIM an gama, wani anguwa neh"
   Ba tare da tace komai ba ta cire paper da Corper Chris ya bata ta mika masa, Kamalu badd yace
    "Haba KIM kinsan ni ban iya abun ku na boko ba kawai karanta mini"
   Batare da tace komai ba ta bud'e paper ta karanta _shagari low cost house A no34_ ga number wayan shi akasa
     Kamalu badd ya bud'e baki yace "Kutt KIM, kinsan Shagari lowcost anguwan soldiers (sojoji)neh koh, kuma gaskia bazan 6oye miki ba tsoron sodoji muke,ga 'yan anguwan sunsan bariki basa tsoro,  kafin a shiga anguwan ma suna checking kar su kama mu tun a gate
       Dariya Khairiyya tafara tace
   "Kai ban ta6a sanin kana da tsoro ba sai yau, amma ka bani kunya Wlhy, kar kaji komai zamu sake musu kud'i idan kud'i batayi aiki ba ma gubza dasu, balle ma nasan cash zaiyi aiki, shiga motar ku kawai mu tafi"
    "Angama Hajiya KIM"
          Ya Khairiyya zasu kare a anguwan sojoji da  Coper Chris,
         Ku biyo mu

 *{```Page 14~16```}*
        Hanyan Shagari lowcost suka kama, nan da minti goma suka isa dan gudun da sukeyi, a bakin gate wasu sojoji neh sun saka bak'in glass fuskarsu a murtuke kamar wanda aka musu mutuwa, Khairiyya ce a gaba su Kamalu badd a bayan ta, Glass na motar ta ta sauke, wani bak'in soldier neh yace fito ki bud'e boot naki, ba musu tafita tana tafiyar ta mai d'aukan hankali ta bud'e boot nata, dubawa yayi yaga ba komai sai spare tyre, duk sojojin kallon ta suke dan Khairiyya ta d'auke musu hankali, sojan murmushi yayi yace
     "Baby mei sunan ki"
   Tana mai mayar mishi da murmushi tace "KIM"
  Yace "Wow nice name, you are so beautiful"
    "I know " shineh kawai abun da ta furta tashiga motar ta, sojan nan haka ya bita yace
   "Ki tsaya muyi magana mana"
   Khairiyya tana mei kallon sa ba yabo ba fallasa tace
   "Dont worry yanxu ina sauri yayata tace na kawo mata carpenters kaga suneh a bayana so please ba sai ka duba suba idan zamu fita zan tsaya muyi magana handsome"
     Kiran shi handsome da tayi ba karamin dad'i ya mishi ba, sai washe hakura yake kamar mai tallan close up yace
    "Ok ok no problem I will be here waiting"
     Tace alright then sai mun fito, ta fisga motar ta ciki su Kamalu bad suka bi bayanta, Line A yana can ciki ciki haka dai suka shiga, suna duba koh wani numban gida, dan kowani gida an rubuta numban a waje, suka samu A36 suka zagaya sukaga A34
     Wayan ta ta cire ta latsa numban shi, ringing d'aya ya d'auka wayan
    Khairiyya tace
    "Hello Corper Chris it's me KIM"
   Daga can Corper Chris yace "Ohh the damsel Kim, i've been waiting for you since, where you at"
    Khairiyya tayi murmushin mugunta tace "At the door sir, can I come in"
    "Sure Damsel Come In, fell free dear"
    Tace "ohk"
 Ta katse wayan, juyawa wajen su Kamalu tayi tace ku shiga bayan minti d'aya, suka ce an gama Kim
      Tura kofan tayi ta shiga, ba laifi gidan tsab sai d'an warin toilet da yake tashiwa, washe hakora yake yana cewa
    "Welcome Damsel, welcome"
   Ya bud'e mata hannu alaman ta rungume sa
   Kau da kai tayi tace "I am tasty"
   "Ohhh sorry pls lemme offer you drinks but before then have a seat" nuna mata kujera yayi ta zauna ya bud'e fridge ya ciro faro water da Coke na roba, kan ya ajiye a gaban ta su Kamalu suka shigo gidan
     Corper chris sai ganin maza karti yayi akan sa da kayan aikin su, muryan sa na rawa yace
   "Who are you, What do u want? "
Kamalu neh ya amsa yace
   "Uwaka da Ubanka neh"
   Khairiyya ta fashe da dariya Coper chris ya juya yana kallon ta with suprise on his face yace
     "Why Kim, Why? "

     Dariyan ta tacigaba tace
"Ohhh Corper Chris you love catching Fun right, we gonna catch some fun now"
   Muryan sa yana rawa yace "what do u mean by that, Please Kim I beg of you don't do anything stupid"
     Su Kamalu bad da yaransa suma sai dariya suke masa dan kusan duka basuji mai suke cewa ba
      Zaiyi ihu Kamalu ya kai masa bugu bakin sa, Khairiyya tace
   "Ahswear Chris don't you dare try that, bamu fara catching fun ba but you are already looking like a fish who has mental issues, ohhh you are such a frickle doodle"
    D'aura shi sukayi da igiya mai karfi hannun shi da kafan shi, gum mai karfi suka manna bakin shi dashi
      Khairiyya tace "Wow I'm gonna enjoy this"
   Shiko duk an d'aure shi ga baki an toshe ba abun da yakeyi sai hawaye
    Dukkan su dariyan sa suke Khairiyya tace
     "We ain't even started, save your tears for letter durling"
       Zuwa wajen fridge nasa tayi ta d'auko ruwa masu sanyi ta watsa masa a jikin sa, sai shure shure yakeyi, gashin kansa daman yatara gashi irin na gayu Razor Kamalu bad yacire sabowa yasaka sabulu da ruwa akansa yafara masa aski, gabad'aya yabi ya 6ata masa kansa kaca kaca
        Wani k'aton bulala Khairiyya ta d'auka ta fara zane shi da bulala tana cewa
     "Ohhh I love this, this is fun, no more than that,  ohhhh" sanda hanun ta yagaji ta barsa, tace Kamalu mu barsa haka atleast yayi catching Fun yanxu, kuma nasan bai ta6a catching Fun irin na yau ba en it will stuck in his brain forever
       Corper dai sai hawaye dan kuka ma bazai iyayi ba dan an rufe bakinsa,Khairiyya tace
  "Tell nobody, Idan kafad'a hmmm i'm gonna rip off your head en then feed it to your bitches" taja tsoki 
 Khairiyya da mutanen ta suka barshi a wajen suka shiga motar su, fitan su a gidan wani yagansu ya shigo da gudu yaga Chris a d'aure, neman wuk'a yayi ya kunce sa ya bud'e masa baki, yace
    "Brother Chris what happen"
    Kasa magana yayi Chris sai neman wayan sa da yake, yana samuwa ya danna wani numba an rubuta my brother, latsa number yayi yakira
    Ana d'aukawa Chris ya fashe da sabon kuka yace
    "Broh m finished, some people came en beat me up, don't allow them out of the gate pls broh, don't let them go" ya kara fashewa da kuka dan yaji zafin dukan da Khairiyya ta masa, ga naushin da Kamalu yamasa sanda bakin sa ya fashe
        Yayan yace "what type of car Chris"
   Chris yace "i don't know lemme ask Gabriel"
   Ya juya wajen Yaron da ya taimaka masa yana hawaye yace
  "Abeg Gabriel what type of car do you see them with"
  Wanda aka kira da Gabriel yana d'an tunani kan yace
   "Yes the guys with Odesys en the babe with S-Cross"
    A take ya fad'awa yayan nashi, yayanshi d'aga kai da zaiyi ya kalla motan sun kusan zuwa gate d'in, a take ya tashi yana ihu yana cewa
    "Don't let them out" da karfin sa, duk sojojin suka tashi suka tsaya bakin gate d'in sukayi cracking gun  (gyara bindigansu) hankalin su atashe duk a zaton su an kawo musu attack neh
     Su Khairiyya sai gani sukayi sojoji sun seta bindiga akansu, gaba d'aya sun tsorata

 *```{Page 17~18}```*
            Su kamalu sun tsure, fitsari neh kawai basuyi a wando ba, sai zufa suke duk AC da yake tashiwa a motar, dan su a rayuwar su suna tsoron sojoji balle sunga sunyi cracking bindigan su, d'aya daga cikin boys na Kamalu yace
    "Wayyo Allah nashiga uku, wayyo Mamata idan sun kashe mu sun kashe banza fa Kamalu"
  Kamalu kam kasa cewa komai yayi duk jikin sa yana 6ari, ba abun da suke ambato wa sai "wayyo"
       Khairiyya ma tayi mugun tsorata, zuciyan ta sai tafasa yakeyi, sai "Inna lillahi wa Inna ilayhir Raji'un" take nanatawa idan sun har6e tama da sunan Allah a bakin ta
 
     D'aya daga cikin sojan neh ya tambaye broh na Chris yace
   "O'boy what happen, who are they"
  Yayan Chris yace
    "Sun ma Chris duka" a irin hausan shi da baiyi kwari ba, wasu sojojin tsoki sukaja wasu kuma sun nufa wajen Khairiyya
  Tsawa suka daka musu
   "Oya come out before we shoot you"
   Jikin ta yana rawa ta fito a motar ta su Kamalu ma suka fito, duk kallon ta sukeyi d'ayan yace
   "Ba ke bace d'azu kika shiga"
   Tace "Yes Sir"
  Yayan Chris yace "All of you go on your kneels now"
    Duk suka zube kasa, Khairiyya ce tayi karfin hali tace
   "Bakusan mei yafaru ba kawai zaku d'aura mana laifi, ni gaskia ba wani kneel down da zanyi, kun san ni wacece?" ba karamin karfin hali tayi ba tafad'a, sai jinjina wa kanta take
   Brother na Chris yace
    "I don't care who the hell are you just go on your kneels"
    Wasu sojoji suna basa hakuri akan ita mace ce wasu suna zigasa ai ta raina su neh, su Kamalu har sun fara shan duka, wata bak'ar mota ceh had'adde da hilox biyu d'aya a gaba d'aya a baya ya dunno kai zuwa gate d'in, gaba d'aya suka tsaya ba matsowa suka sara wa motoci ukun
     Sojan gaban cikin jeep ya fito ya bud'e bayan, wani saurayi neh mei jini ajiki wanda bazai haura shekaru talatin da biyar ba, baza kira sa dogo ba amma shi ba gajera ba madai daici mai faffad'ar kirji da gani yaci gym, kalan sa irin chocolate colour mai kyau, yana da ido daidai da hanci wanda ya dace da fuskar sa, ga bakin shi karami sai saje wanda ya kwanta luff a kyakkyawan fuskar shi, fuska a murtuke ya fito a motar yana kallon Khairiyya da sojojin yace
    "What's happening here"
    Duk sun rud'e suka ce
  "Nothing Sir"
    Ya juya wajen Khairiyya yana kallon ta yace
    "What are you doing here"
     Kallon sa Itama take, a jikin uniform nasa taga an rubuta *Captain Suraj a.a*, muryan ta yana rawa dan tayi matukar tsorata dashi tace
    "Sir One of them try to rape me, a garin kare kaina shineh yaji ciwo and kuma shineh zasu mini duka nima"

     "What! Ya juya yana kallon su" duk hankalin su ya tashi, ya kara juyawa yana kallon ta, ita kuwa sai zare zaren ido takeyi, yana ganin ta yasan sharri take musu dan shi yana iya ganeh gaskiar mutum da wuri
    Yace "you can go now"
  Ta juya wajen su Kamalu wanda suka d'an sha bugu tace tashi mu tashi
    Ta 6angaren captain Suraj kuma mamaki yakeyi, wannan wace irin yarinya ce karama batajin magana tasa kanta acikin masifa bata tsoron abunda yan iska sojoji zasu mata yace
    "Zamu raka ki gida"
  Ya juya wajen sauran sojojin yace
    "Idan nadawo zakuyi explaining abun da kuke so ku mata, stupid"
   Aka bud'e masa mota ya shiga, su Khairiya ma suka shiga motar su, bayan ta suke bi, dan su Kamalu sunyi hanyan su daban, ita Khairiyya zuciyan ta na tsinkewa wai meisa dole sai ya biyo ni neh koh bai yadda da ni baneh, haka dai har suka karaso anguwar su wanda yake Circular Road, daidai tazo gate ta tsayar da motar, ta fita aciki shima Captain Suraj aka bud'e masa kofa yafita
     Ya samei ta a inda take tsaye yace
    "Ke daughter'n Alh Ibrahim Muhammad fu'ad mai naira neh"
   Tace "Eh"
  "Be carefull next time dan bakisan da irin mutanen da zaki had'u ba, dan daga ganin ki nasan ke kika ta6o su"
   Khairiyya tace
  "Nifa ban ta6o suba su suka fara" tana tura baki, hakan da tayi ba karamin kyau ya mata ba, kallon ta kawai yakeyi baya kifta ido, azuciyar shi cewa yake
   "Yaa salaam Allah mai iko, irin wannan halittar"
   Haka ta karashe maganar yana kallon ta, ita kuwa da ta lura haka ta buga masa hannu tace
   "Hea you Suraj, what are thinking"
  Yadawo hankalin sa yace
   "Nothing, zan na zuwa dubaki In Shaa Allah duk time da nake maiduguri, do take care of yourself please"
    Tana murmushi a fili amma can cikin zuciyan ta cewa take mtsw Mallam yi sauri ka tafi dallah na tsana shishshigi, tace
  "Ohk I will, bye"
   Ya juya zai tafi Itama zata shiga motar ta yace
  "emm please can I have your digits"
  Tace"sure why not"
  Ya mika mata wayar sa ta saka numban ta, a take yayi dialing yashiga, yace save my number please
 "Don't worry I will, thanks" ta shiga motarta ta danna horn da karfi aka bud'e mata gate, shiko yana so ya tambaye sunan ta amma yakasa
   Tana shiga gida ta fad'a parlour ta zauna akan kujera tace
   "Wayyo Allah what a Day! munyi catching Fun sosai wow" sai dariya take idan ta tuna da Corper Chris da Kamalu yadda suka tsure da sukaga sojoji sunyi cracking bindiga, darawa take kamar wata zararriya, can bayan tagaji tafara ihun kiran masu aikin ta dan da tashigo bata gansu ba, atake duk su ukun suka fito, Khairiyya tace
  "Wai bakuji na shigo baneh baza kuzo ku mini sannu da zuwa ba, tukunna ma uban mei kukeyi a ciki"
    Duk sun tsorata dan kallon film sukeyi aciki wanda ya d'auke hankalin su basu san lokacin da tadawo ba, Haule neh tayi karfin halin cewa
   "Hajiya kiyi hakuri kallo mukeyi bamuji ba"
  Kallo ta watsa musu kan tace
   "Ya muku kyau toh, Dije mei kika dafa"
   "Hajiya pepper fish da soyayyan doya"
   "Bana so bazan ciba, had'a mini hamburger da pickles kafin nayi wanka nafito"
    "Toh Hajiya angama" cewar Dije
   Khairiyya ta juya wajen Indo tace
    "Ki gyara mini d'aki nah na upstairs zan koma can yau so kikai mini duk abun da is important can d'akin nagaji da kwana a kasa"
   "Toh Hajiya" cewar Indo
   Ta kara juyawa wajen Haule tace "had'a mini ruwan wanka yanxu" itama Haule ta fice

      Saurayi neh fari sol wanda bazai haura talatin ba koh ishirin da tara,  kwance akan katuwar gado, idon sa arufe wanda yasa na kare masa kallo sosai, yana da dogayen eyelashes da gira kamar wanda aka zana bak'i sosai, ga hancin sa dogo kamar pencil sai bakin sa karami pink kamar wanda ya saka jan baki, ga sajen fuskar sa baki shima wanda ya dace da kalar sa,gashin kansa bak'i da d'an tsayi, fuskan nan wani waje yayi jaa zur haka ma jikin sa, da ganin alama duka aka masa
    Bud'e d'akin akayi, wata mata wanda baxata haura shekaru hamsin ba tashigo, ko ba fad'a ba ansan jinin sace dan kamanni da suke, sai dai duk da haka tafisa haske, ta zauna kusa da shi tace
   "Haba Zilyadeen, mei yayi zafi haka, tun ranar da abun yafaru baka magana baka cin abinci, meisa baka da hakuri neh just forgive en forget"
    Bud'e idonsa yayi wanda ni Nana I was shock, idonsa manya manya fari kal dashi, Yace
  "Mummy bazan ta6a forgetting  ba not to talk of forgive, taci mini mutunci ta ciwa Inna mutunci, ba yarinyan Fu'ad mai naira baneh, ai baza ta 6oya ba, zan koya mata hankali mummy, mummy sai ta.... "
    Bai karasa maganar ba tasaka yatsan ta a lips nashi, tace
    "Shhhhh Zil, idan har ni na haife ka toh Forgive en forget, idan kana kauna ta ka yafe mata ta kacire wannan abun a zuciyar ka"

 *```{Page 19~20}```*
          Ba yadda ya iya dole yace "Mummy shikenan In Shaa Allah zan manta, but kinsan is not easy na manta da wuri, but I will try my very best na manta"
    Mummy tayi murmushi tace "Yawwa thank you son"
      Yanxu ka tashi kaci abinci kasha magani, ka duba yadda ka rame fisabillah sabida kasa yarinyan nan a ranka, ai haka bashi da anfani, maza ka tashi gashi na saka an kawo maka abinci har d'akin ka kuma your favourite food na dafa maka
   Haka ya tashi ta tura masa abinci a gaban sa tana gadin sa dan dole sanda yaci yasha magani, mummy tace Haba koh kaifa, kabi kasaka abun da bashi da anfani a ranka
     Shi ko Zilyadeen Allah kad'ai yasan yadda yake ji aransa, yarinyan da bazai ta6a mantawa a life nasa ba, taci mutuncin sa en most off all his belove Grandmaa d'inshi, sosai idan yatuna ta zuciyan shi yake k'ona, Mace da shaye shaye kai Allah wadaran

       Khairiyya zaune a garden tana shan strawberry tana karatu, wayan ta neh ya fara ringing, duba screen tayi taga Abba, da shagawa6a ta d'auka wayan tana mai tura baki tace
  "Abba ina missing naka"
Daga can Abba yace kar ki damu very soon zaki ganni, ya kike da kuma karatu
 "How can I be fine Abba, kullum ni kad'ai ba kowa kusa dani sai wayannan masu aikin daka had'ani dasu, they are so boring"
    Kar kidamu daughter very soon zan zo
  Abba en this time idan kazo dole kayi aure dan ni gaskia nagaji da zama ni kad'ai kamar mayya
   Abba yayi dariya yace "Toh shikenan worry not dear idan nazo ke da kanki zaki za6a mini matar da zan aura"
  Khairiyya tace "yawwa Abba kokai fa yanxu naji magana"
   Abba yana dariya yace toh yanxu zan tura miki wani number sai ki tura jamb registration number ki da all the details da yake kan slip d'inki kinji
   Khairiyya tace "yes Abba za'a mini abu kenan" tana dariya
    Bance ba just read kar kice baza kiyi karatu ba dan ba taimaka miki za'ayi ba, wani university kikayi applying neh
   Tace Abba "Unimaid mana"
 "Haba mei zakiyi da unimaid I tot koh Baze koh Nile zakije"
   Khairiyya tace
"Aa Abba ni Unimaid nakeso banso nayi nisa da gida, kai baka nan, Ammi batanan toh wa za'a bari a gidan"
  Jin ta ambato Ammi yace bye take care sai na kara kira, tace ohk Abba Thank you
    Bayan kwana biyu da rubuta Jamb Khairiyya tana zaune a d'akin ta tana kallon GOT (game of thrones) dan tana bala'in son series d'in tana cikin kallo taji text yashigo mata wayan ta, bud'e wa tayi to her suprise taga Jamb, da sauri ta bud'e text din zuciyan ta yana bugawa, Ihu ta sake mai karfi wanda ni Nana ya firgita ni, OH EM GEE I can't believe this, Allahu Akbar, Allah nagode maka har nakai 235 scores, what a miracle" dad'i taji kamar azuba mata ruwa a kasa tasha tace
  "Atlas nima yanxu zan daina saka uniform, wai za'a dama da mu a jami'a"
 Atake ta d'au wayar ta ta latsa num Abba, yana d'auka wa tayi wani ihun har sanda yaji kiiiii a kunnan sa,  tace
     "Abba guess what"
  Abba yace Tell me dear it seems like you are in a good mood 
  Khairiyya tace "more than good Abba, I pass my Jamb" tayi wani ihun 
  Abba yace "wow so happy for you baby, yanxu mei kike so na siya miki"
   Khairiyya tace nidai Abba idan na samu admission mota nake so a canza mini
   Abba yace "Haba mota kuma, bayan duk motocin da suke gidan, motoci nah ma naga duk ke kike using"
    Tana tura baki kamar yana kallon ta tace
"Abba gaskia motocin ba wanda ya mini, duk old model neh"
   Abba ya numfasa kan yace "Toh yanxu wace irin mota kike so dear" atake tace FERRARI Abba new model koh BMW e-class27
    Abba yace kwantar da hankalin ki kamar kin samu, tayi ihu tace thank you Abba
 Tana gama waya da Abba taga wani sabon number yana kiranta, kamar baza ta d'auka ba haka ta bari ya katse, wayan still ya sake ringing same number, d'aukar wayar tayi tace haba dan Allah idan mutum an kirasa bai d'auka ba sai ya hakura ai,bawai ata kiraba mtseww who is on the line
    Shiru akayi ba amsa tasake cewa wai wannan wani irin iskanci neh zaku kira mutum kuyi shuru
    Daga 6angaren wanda ya kira da husky voice nasa yace *Captain Suraj* neh
     Baki ta bud'e ta kasa cewa komai, ya kara cewa
 "Hlo kinaji"
Tace "yes, wa kake nema"
Cap Suraj yace "m I not talking to emmmm" dan baisan sunan taba dan bai tambaya ba lokacin
  Khairiyya tsab ta ganeh neh shi tace
  "Sorry wrong number, en please kar ka kara calling dan matar aure ce ni" kat ta katse wayan tana wayyo Allah ina ni ina soldier ai yafi karfina
   Shiko ta 6angaren sa murmushi yayi dan yaganeh muryan ta and kuma time da tabasa yayi dialing agaban ta kuma ya shiga ya gani da idonsa
      Khairiyya tace wow Game of throne sorry zan fita dan Jamb nawa yafika,  Wow this call for celebration dole nayi celebrating, kashe laptop nata tayi ta fad'a toilet tayi wanka, bud'e jibgegen wardrobe nata tayi wanda ya cika da kayan sawa designers kala kala daban daban, wai yanxu wanne zan saka

 *```Page 21~23```*
            Wata doguwar habbaya bak'i ta saka da touches blue a saman, tayi rolling da vail nashi, yau powder da lipgloose da mascara ta shafa batayi heavy makeup ba, ta saka takalmi high heel black yana da touches blue da Jaka black, ta d'auka  key mota
      Hanya kicin direct tabi tashiga, ta kalla Dije tana wanke wanke, tace
 "Dije ku shirya dake dasu haule na kaiku shopping"
Dije ta washe hakora tace Toh hajiya, ta wanke hannun ta tace hajia bara na musu magana, d'aga kai Khairiyya tayi tace
"Toh Wlhy na baku minti biyu idan baku fito ba zanyi tafiya ta" ta juya tabar kicin d'in
      Fita tayi harabar gidan wajen parking space, wata bakar 4matic mota tashiga, wow motar ta kar6e ta ba karya, kafin ta rufe kofa har su Dije sun fito, suma suka shiga motar, gaishe ta sukayi tayi kamar bataji ba,Khairiya  tace
"Kar ko wacce tayi siyayyen sama da dubu talatin, toh nidai na fad'a muku"
  Duk suka had'a baki sukace
"In Shaa Allah hajia"

       Babbar Mall suka shiga, ko waccen su sai duba abin siya take, Khairiyya kuwa tana wajen agogo da bangles, tana cikin dubawa taje an tab'a ta tabaya, ba tare da ta juya ba tace
"Toh menene kuma, kar ko wacce acikin ku nace tayi siyayyan sama da dubu talatin, idan kudin ya haura toh bazan iya biya ba" ta cigaba da duba bangles d'in, aka kara tab'a ta tabaya, juyawa tayi a fusace tace
 "Wai wani irin iskanci neh ha..," bata karasa cewa haka ba tayi ido hud'u da wani yaro fari wanda akalla bazai wuce 22yrs ba, yana da matsanancin tsawo,da kananan ido, sai baki karami amma bak'i kirin, yana murmushi yace
"Oppps sorry baby, I really just can't stop maslf but you are Hot"
  Harara ta watsa mishi tace "I know ama Hot so please can u excuse me"
    Yaron yace "Haba baby wannan ai ba class naki baneh, by d way sunana Sabir, ina karanta Info Tech a Malaysia yanxu haka hutu nazo"
   Khairiyya tace "Sorry dude but ban tambaye ka ba, so why kake fad'a mini, I have nothing to do with that and please karka saka mini ciwon kai kabar nan"
  "Baby I got Cash, zan iya baki ko nawa en I can buy any damn thing for u" cewar Sabir
  Khairiyya tace "toh Mallam I ain't interested, koh ce maka akayi banda kud'i, Wlhy saidai na baka badai kai ka bani ba, stupid jerk"
   Bangaje shi tayi ta wuce, ta same Indo tace maza suzo siyayyan ya isa haka, basu gama ba dole suka bar mall d'in, Sabir bai hakura ba har wajen motar ta yaje yace
 "Haba baby sonki dagaske nake koh number wayan ki kibani please"
   Khairiyya bata kara cewa komai ba ta fisga motar ta tabar wajen
      A yau su Khairiyya zasu koma makaranta dan hutun jamb da aka basu yakare, Haule ce tashiga d'akin Khairiyya dan ta da ita a barci, kwance take akan tile na d'akin akasa, ta dunkule da alama tana jin sanyi dan ga sanyi AC har biyu, ga iskan fan ga kuma sanyin tiles, tana sharan baccin ta ga kwalaben syrup har uku a kasa, Haule sai bubbuga ta take tana cewa
 "Hajiya ki tashi yanxu fa karfe bakwai da rabi zakiyi latti" Khairiyya kam sai baccin ta takeyi, haka Haule ta cigaba da bubbuga ta har sanda ta tashi, da muryan bacci tace
 "Wai ni Haule kee wace irin mutum ce ina bacci zakizo kina tadani ehh, ai wannan rashin hankali neh"
"Hajia kiyi hakuri naga zakiyi lattin makaran ta neh shiyasa na tashe ki" cewar Haule
 Khairiyya ta harare ta tace
 "Toh ina ruwan ki da makaranta na, nifa shishshigi neh bana so"
   Hajiya kiyi hakuri cewar Haule, Khairiyya tana kumbure kumbure ta tashi ta shiga toilet, bayan minti uku sai gata ta fito, a gurguje tayi shirinta ta d'auka motar ta 4matic baka tafita dashi, tana kan titi taji ana mata horn da karfi, ta duba ta mirrow motar ta taga wata Benz blue tana binta, birik taja ta tsayar da motar, wanda ke cikin motar ya sauka a motar, ba kowa baneh illa Sabir, wanda suka had'u a mall, tana ganin shi ta madubin motarta taja wani dogon tsoki
   Zuwa wajen motar yayi yace
"Baby gashi Allah ya kara had'amu, please number ki nakeso da address naki please"
   Khairiyya ba karamin haushi ya bata ba tace
"Idan na baka uban mei zakayi dashi"
"Haba Baby zan na kiranki ina jin swt voice naki mana, the 1st tym I saw you I fall in love with you, love at 1st sight kenan please just give me your digits"
   Dogon tsoki Khairiyya taja tace
"Toh bazan bayar ba, ana dole, kaga ka matsa mini a hanya koh na buge ka, idan na buge ka na buge banza kasan nayi lattin school koh"
    Sabir gaban motar yaje yace
"Sai dai ki buge ni, I love you, I so much love you, to the end of infinity, I can kill for you, I can die for you, idan kin buge ni na mutu ba matsala sabida ina kaunar ki, ina mutuwar sonki


No comments

Powered by Blogger.