Boko Haram na iko da kananan hukumomi 17 a Borno - Sani Zoro
Sojojin Najeriya sun yi ikirarin murkushe Boko Haram |
Wani kwamitin majalisar wakilin kasar ya ce har yanzu akwai yankunan jihar Borno da ke karkashin ikon mayakan Boko Haram.
Kwamitin ya yi wannan ikirarin ne bayan wata ziyarar aiki da ya kai a shiyar arewa maso gabashin Najeriya da ke fama da matsalar Boko Haram.
Shugaban kwamitin majalisar a kan masu gudun-hijira, Hon. Sani Zoro wanda ya jagoranci tawagar ya shaida wa BBC cewa har yanzu tsugune ba ta kare ba a yakin da sojojin kasar ke yi da Boko Haram, duk da ikirarin da suke yi cewa sun karya-lagonsu.
Ya ce 'Yan Boko Haram sun mamaye Kananan hukumumi 17 da suka hada da Abadam da Kalabalge.
"Suna cin karensu ba babbaka suna karbar haraji."
"Suna tilastawa mutane a tara masu kudi su kuma dawo su karba. Idan an ce ba su ke rike da ikon wadannan wuraren ba a gwamnatance to karya ne," in ji shi.
Ya kara da cewa saboda barazanar Boko Haram a Kalabalge ne ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta yanje jami'anta na agajin gaggawa.
Wannan dai ya ci karo da ikirarin rundunar sojin Najeriya da ke cewa babu wani bangaren kasar da ke karkashin ikon Boko Haram.
Hon. Sani Zoro ya bukaci Buhari ya dinga kai ziyara Borno. |
Amma Hon Zoro ya ce "gara su daina fadin haka domin mutanen da abin ya shafa su suka san halin da suke ciki."
Ya sun tafi garin Bama a ranar 5 ga watan Nuwamba inda suka zagaya sassan garin kuma abin da suka gani ya nuna tsiraru ne akwai a garin da ba su kai mutum 200 ba.
"Ko angulu babu a gidan sarkin Bama duk an watse."
Kwamitin ya yi kira ga shugaba Buhari ya dinga kai ziyarar ba-zata a Borno da kansa, kuma ya dage kan sai an kai shi wuraren da aka ce an kwato daga hannun Bko Haram
Sannan a gudanar da kwakkwaran bincike game da ayyukan tsaro a yankin na arewa maso gabas.
No comments