Fabregas zai bar Chelsea, Barca na neman Kompany da Ivanovic
Dan wasan tsakiya na Chelsea Cesc Fabregas, mai shekara 31, ya ce zai ci gaba da taka leda a kulub din har karshen kaka da kwangilarsa za ta kawo karshe, amma ya ce yana ganin za a yi ribibinsa idan an bude kasuwa a Janairu, in ji (Talksport).
AC Milan tana nazarin karbo Fabregas daga Chelsea da shi da Christensen kamar yadda Jaridar (Gazzetta dello Sport - ta Italiya) ta ruwaito.
Fabregas ya koma yana cin benci, tun zuwan sabon kocin Chelsea Maurizio Sarri, inda tun fara kakar bana ba a fara wasa da Fabregas ba a Chelsea.
Dan wasan tsakiya Jorginho da Chelsea ta karbo kan fam miliyan 50 ne ya benci Fabregas a Stamford Bridge.
Fabregas dai na ganin zai samu dama a wasannin da Firimiya da za a buga a lokacin bikin kirsimeti.
Barcelona kuma tana tunanin karbo dan wasan Manchester City dan kasar Belgium Vincent Kompany da kuma dan wasan baya na Zenit St-Petersburg Branislav Ivanovic na Serbia domin kara wa bayanta karfi, in ji (Mirror).
Rahotanni daga Spain sun ce Barcelona tana neman sayen kwararren dan wasan baya ne da za ta karbo a watan Janairu saboda dan wasan Samuel Umtiti da ke fama da rauni.

No comments