Buhari ba ya karya –Ministar kudi
Zainab Shamsuna ta ce gwamnatin Buhari tana sane cewa 'yan kasar na fama da wahala |
Ministar kudin Najeriya ta Zainab Ahmed ta kare shugaban kasar Muhammadu Buhari kan ayyukan da ya ce gwamnatinsa na aiwatarwa sa'ilin gabatar da kasafin kudin kasar na 2019, a zauren majalisar dokokin kasar.
Ministar kudin ta ce babu yadda za a yi shugaban kasar ya fadi abinda ba gaskiya ba ne.
A cewar ta "Shugaban kasa mutum ne mai gaskiya kuma tsayayye, ba yanda za a yi ya ce an yi abu wanda ba a yi ba."
A cikin hirar da ta yi da BBC, ta ce dukkanin ayyukan da shugaban kasar ya fada suna cikin kasafin kudin shekarar 2018, wanda zai tsaya a watan Yunin shekarar 2019.
Ta kuma ce an sake sanya ayyukan cikin kasafin kudin shekarar 2019, domin tabbatar da cewa an kammala su.
An dai samu rudani a lokacin da shugaban ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a zauren majalisar dokokin ta Najeriya.
Inda wasu wakilan majalisar suka rinka katsalandan a lokacin da shugaban kasar ke jawabi, musamman a lokacin da yake bayani kan nasarorin gwamnatinsa.
Sun rinka cewa 'karya', ko 'a ina?', wasu kuma na cewa 'ba haka ba ne.'
No comments