Abubuwa 5 da Atiku zai sa a ransa kafin ya ci zabe
Atiku Abubakar dan takarar mukamin shugaban Najeriya a karakashin jam'iyyar PDP |
A yayin da Najeriya ke shirin gudanar da zabukan 2019, ga wasu abubuwa da dan takarar jam'iyyar PDP mai adawa da gwamnati ya kamata ya yi domin samun nasarar lashe zaben 2019.
1. Nisanta kai da jam'iyyarsa
Masana kamar Farfesa Umar Pate da Mohammed Jega na ganin tilas ne Atiku Abubakar ya sauya tunanin da al'ummar Najeriya ke yi kan kaurin sunan da jam'iyyar PDP ta yi na rashin cika alkawuran da ta yi wa 'yan kasar a tsawon shekaru 16 da tayi tana mulkin kasar.
"Wannan babban tabo ne da jam'iyyar ta PDP ke da shi, kuma zai fuskanci kalubale wajen gyara barnar da aka tafka a wancan lokacin," inji Farfesa Umar Pate.
"Saboda haka yake bukatar raba gari da yadda wadancan gwamnatocin suka tafiyar da mulkin kasar," in ji Farfesan
Ya kara da cewa: "Akwai kuma batun gamsar da 'yan kasar cewa dukkan abubuwan da suka auku a karkashin mulkin jam'iyyar PDP ba za a sake bari su auku ba nan gaba.
"Wannan abu ne mai wahalar samu, amma yana cikin manyan matsalolin da ke damun jam'iyyar da ta zabi Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa," in ji shi.
Ga kuma abin da Mahmud Jega ya ce a kan wannan batun:
"Atiku na bukatar nisanta kansa da yadda jam'iyyarsa ta PDP ta wawure baitulmalin kasar, misali yadda ta karkatar da kudaden da aka ware domin sayen makamai da aka shirya yakar kungiyar Boko Haram da su.
2. Sauyin alkibla
Mahmud Jega ya kara da cewa, "Dole ne dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa zai kaucewa halayyar nan ta yadda aka rika watanda da kudaden kasa a lokacin da jam'iyyarsa ke mulkin kasar."
Mahmud Jega cewa ya yi dole ne Atiku Abubakar ya gamsar da jama'a cewa zarge-zargen da ake masa na cin hanci da rashawa babu kanshin gaskiya a cikinsu |
Masu lura da harkokin siyasar kasar sun ce yadda aka rika facaka da dukiyoyin al'umma ya taimaka wajen rusa tsarin tattalin arzikin Najeriya bayan ta shafe shekara 16 a karkashin mulkin jam'iyyar ta PDP.
Rashin iya taka wa gwamnatocin jihohi da kuma rashin tsawata wa jami'an gwamnati da aka samu da laifin karkatar da kudaden al'umma.
Dole ya kuma nuna wa duniya cewa zai ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar aiwatar da matakan da Shugaba Buhari ya fara fi wajen yin hakan.
Farfesa Umar Pate na jami'ar Maiduguri na cikin wadanda su kayi tsokaci:
"Atiku Abubakar na da dama babba idan zai iya gamsar da 'yan Najeriya cewa zai magance wasu daga cikin matsalolin da suka addabi Najeriya, kamar batun ayyukan raya kasa."
Shi kuma babban dan jarida Mahmud Jega cewa yayi dole ne Atiku Abubakar ya gamsar da jama'a cewa zarge-zargen da ake masa na cin hanci da rashawa babu kanshin gaskiya a cikinsu.
"Lallai ne ya kuma sauya tunanin mutane da ke cewa Amurka ta hana shi shiga kasar saboda ana tuhumarsa da aikata laifin da ke da alaka da cin hanci da rashawa."
3. Tattalin arziki
Dole ne Atiku Abubakar ya nemo hanyoyin bunkasa tattalin arzikin Najeriya, musamman ta bangaren samar da ayyukan yi da abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi da gine-gine.
A bangaren sufuri, Najeriya na bukatar hanyoyin jirgin kasa, da gyaran manyan hanyoyi da kuma inganta sufurin jiragen sama.
Idan zai iya tabbatar wa mutanen kasar cewa yana da shirin inganta tattalin arzikinta, yana iya samun galaba a kan gwamnati mai ci.
A matsayinsa na dan kasuwa, zai taimakawa sosai wajen ganin an ci yar da tattalin arzikin gaba, a cewar masu sharhi kam al'amura a Najeriya.
A bangaren sufuri, Najeriya na bukatar hanyoyin jirgin kasa, da gyaran manyan hanyoyi da kuma inganta sufurin jiragen sama |
A nan ma, Farfesa Umar Pate ya ce "Tattalin arzikin Najeriya na bukatar garambawul, saboda haka ne Atiku Abubakar ya iya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa zai gyara hanyoyi da makarantu da asibitoci."
Farfesan ya kuma ce, "Wannan ba abu ne mai sauki ba, amma dole ne ya fito ya nuna wa 'yan Najeriya yadda zai jagoranci kasa mai dumbin arziki kamar Najeriya zuwa yalwatuwar arziki."
Shi kuma Mahmud Jega ya nemi Atiku Abubakar da ya fitar da wani shirin gyara ga tattalin arzikin kasar:
"Ya kamata ya nuna wa mutane yadda zai yi gyara ga tattalin arziki musamman yin wasu ayyuka da gwamnatin Buhari ta gaza aiwatarwa."
4. Yaya za a yi harkokin ilimi su inganta
Harkar ilimi ce ke kan gaba a yawancin sassa na duniya amma kuma an bar Najeriya a baya.
Kasa ce mai yawan al'umma da ke bukatar ilimi mai inganci domin kawo ci gaba a fagen kimiyya da fasaha.
Saboda haka yana bukatar ya gamsar da 'yan Najeriya cewa zai dauki matakin inganta harkar ilimi idan an zabe shi.
Idan har yana so har 'yan Najeriya su fito su zabe shi, lallai ne ya tabbatar masu da irin matakan da zai dauka na bunkasa ilimi |
Farfesa Umar Pate: "Idan har yana so har 'yan Najeriya su fito su zabe shi, lallai ne ya tabbatar masu da irin matakan da zai dauka na bunkasa ilimi. Idan aka lura a yanzu, duniya na cigaba kwarai a fagen ilimin kimiyya da fasaha. Ya kamata wanda da zai jagoranci Najeriya ya kasance ya ba wannan fannin muhimmanci matuka."
Mahmud Jega kuwa na kallon batun ne ta yadda Atikun yayi nasarar kafa jami'a a Yola.
Yana ganin cewa Atiku "zai iya jan hankulan jama'a idan ya nuna masu cewa zai inganta ilimi domin dama yana kan hanyar yin haka."
5. Noma da kiwo
"Idan ba abinci ba za a sami zaman lafiya ba. Idan ba abinci hankalin mutane ba zai kwanta ba", inji Farfesa Umar Pate.
Ya kuma kara da cewa "Dole ne Atiku Abubakar ya fito da hanyoyin da za a bunkasa harkokin noma da kiwo."
Najeriya kasa ce mai dumbin albarkatun na kasa da ruwa, inda za a iya gudanar da ayyukan da suka shafi noma da kiiwo da kamun kifi.
Masana sun ce dole ne Atiku Abubakar ya fito da hanyoyin da za a bunkasa harkokin noma da kiwo |
Ana bukatar shugaban da zai jagoranci Najeriya wajen cimma matakin wadatar da abinci ga miliyoyin al'umomin kasar.
Yana da muhimmanci dan takarar ya fitar da hanyoyin da za su gamsar da al'umomin Najeriya cewa idan ya kasance shugaban kasa, yana da shirin inganta wannan fannin.
Mahmud Jega: "Yana da muhimmanci ya samr da wani shiri na kawo karshen rikice-rikicen makiyaya da manoma da ya addabi wasu yankunan kasar, domin wannan zai iya dawo da martabar noma da kiwo a kasar."
No comments