LABARI MAI DADI GA 'YAN SANDA
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da yiwa Albashin jami'an 'yan sanda garan bawul, shugaba Buhari ya amince da hakane domin karawa jami'an kwarin guiwa wajen tabbatar da tsaron cikin gida.
Yayin ziyarar da Shugabannin ‘yan sandan tare da Shugabannin hukumar lura da aiyukan ‘yan sanda wato PSC suka kaiwa shugaba Buhari yau Litinin, shugabannin rundunar ‘yan sandan sun godwwa shugaba Buhari bisa amincewa da ya yi a sauya tsarin albashin ‘yan sanda domin Kari akan albashin su da kuma kudaden su na fansho.
Sai dai shugaba Buhari, ya bayyana takaici kan yadda ‘yan sanda suka gaza sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya dora musu, wanda hakan ya tilasta amfani da sojoji wajen tabbatar da doka da oda a fadin kasar nan.
Ya ce, “Daga Taraba zuwa Sokoto, zuwa kudu maso kudu, mutane basa samun kwanciyar hankali akan hanya har sai sun ga sojoji, Ina farin cikin kara albashin da alawus da fatan zai taimaka wajen bunkasa aikin ‘yan sanda domin tabbatar da tsaron cikin gida.
Shugaba Buhari ya kara da cewar
“Su sojoji kamata ya yi a ajiye su domin tunkarar manyan ayyuka da ka iya tasowa. Akwai bukatar ‘yan sandan su mike tsaye domin tunkarar kalubalen fashi da makami da satar mutane domin neman kudin fansa, a birane da kauyuka. Idan har ‘yan sanda suka zama kwararru kuma jajirtattu, to al’umma da gwamnati zasu samu gamsuwa.

No comments