5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Kisan 'Yan'uwa Musulmi A Abuja Ya Sabawa Dukkan Dokoki, Inji Sheikh Halliru Maraya - Arew@Blog Kisan 'Yan'uwa Musulmi A Abuja Ya Sabawa Dukkan Dokoki, Inji Sheikh Halliru Maraya - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Kisan 'Yan'uwa Musulmi A Abuja Ya Sabawa Dukkan Dokoki, Inji Sheikh Halliru Maraya



Daga Bilya Hamza Dass

Shaikh Halliru Abdullahi Maraya wani fitaccen Malamin Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, ya bayyana cewa, kisan da Sojojin Najeriya ke yiwa 'yan'uwa Musulmi ya saɓawa doka.

Shehin Malamin ya shawarci gwamnati akan da ta buɗe kofar tattaunawa ne da Harkar Musuluncin domin ganin an samar da mafita tare da samar da hanya mafi sauƘi wajen ci gaba da gudanar da muzaharori domin kaucewa rasa rayukan al’umma da dukiyoyi.

Malam Halliru Maraya ya bayyana cewa, "Kotu kadai take da damar yankewa ɗan kasa hukuncin kisa.”

A wani bangare na bayanin na shi Malamin ya yi, ya kara da nuna cewa manyan manufofin kowacce gwamnati shi ne, kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce, "abin bakin ciki ne a ce a wannan zamanin na ci gaba, muna ci gaba da kashewa da wulakanta gawarwakin matasa ‘yan kasarmu. A lokacin da sauran kasashen Duniya ke horas da nasu matasan domin samun kwarewar da za su iya shugabanci a nan gaba".

A cikin wannan makon ne dai Sojojin Nijeriya suka akawa ‘yan'uwa Musulmi a lokacin Tattakin Arba'een na bana a birnin Abuja, inda suka kashe mutane da dama sannan suka jikkita wasu, tare da kama sama da mutane 400.

No comments

Powered by Blogger.