5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda
site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0
Yacce ake miyar kori - Arew@Blog
Yacce ake miyar kori - Arew@Blog
Assalmu alaikum warahmatullah barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka. Yau za muyi miyar kori (curry soup)
Abubuwan hadawa
Kori (curry powder)
Attaruhu
Tattasai
Naman rago
Tafarnuwa
Citta
Albasa
Man gyada
Maggi
Gishiri
Yadda ake hadawa
Da farko za ki gyara namanki ki yanka albasa ki sa maggi da gishiri kadan sai ki daka citta da tafarnuwa ki zuba ki dora a wuta.
Sai ki markada tattasai da attarugu da albasa sai ki zuba akan namanki ki rufe ya samu minti sha biyar sai ki zuba manki, ki soya sama sama.
Idan ya yi sai ki zuba ruwan namanki sai ki zuba maggi tafarnuwa kori idan za ki zuba korin ki sa mai dan dama dan ya yi kala sosai
Sai ki juya shi sosai sai ki dan dana ki ji idan komai ya yi sai ki rufe ya yi minti biyar sai ki sauke. Za ki iya ci da shinkafa ko doya ko sakwara.
-
No comments