LABARAI A TAKAICE GA ZABEN 2019
LABARAI A TAKAICE
*Biyo bayan nasara da tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya samu na lashe zaben fidda gwani na babbar jam’iyyar adawa PDP, yanzu shine kan gaba cikin wadanda za su yi takarar neman shugabancin Najeriya a 2019 in Allah ya kai mu da shugaba Buhari a APC.*
*Atiku ya yi nasara kan ‘yan takara 11 inda ya samu kuri’u kusan ninki 3 da mai bin sa a baya wato gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal wanda ya samu kuri’u 693. Tsohon mataimakin shugaban ya samu kuri’u 1,532. Sauran ‘yan takarar sun hada da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wanda ya zo na uku da kuri’u 317.*
*Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na Gombe ya samu kuri’u 111. Atiku dai ya nuna wannan dama ce ta sake dawo da PDP kan mulki bayan faduwa zabe da ta yi a 2015 inda adawa ta samu nasara a karo na farko a tarihin Najeriya.*
*Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta nuna damuwa abun da ta zaiyana da barin wasu da ba su dace ba su ka karbe nasarar APC a wasu jihohi bayan wasu ‘yan takara sun sayi takardar neman izini da dan Karen tsada.*
*Bayanan da Aisha Buhari ba za su rasa nasaba daga yadda korafi ya fito daga wasu jihohi cewa ba a yi zaben fidda gwani na APC ba ko kuma an bi ta wata hanya da ba ta kan ka’ida wajen fidda ‘yan takarar. Da wannan Aisha ta bukaci ‘yan Najeriya su kaucewa zaben duk wani dan takara mai matsala da ke da muradun da su ka saba da adalcin dimokradiyya.*
*Duk da bayanan na uwar gidan shugaban ba su ambaci zaben jihar ta ta Adamawa kai tsaye ba, ta ce wasu sun shiga zabe inda a ka dau nasarar a ka damka ta ga wasu. Kanin Hajiya Aisha, mai suna Muhammad Halilu Modi na daga ‘yan takarar da ya shiga zaben ba tare da samun nasara ba, inda gwamna da ke gado Bindow Jibrilla ya samu nasara.*
*Tsohon gwamnan Kuros Ribas a Najeriya Donald Duke ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar adawa ta SDP. Duk ya yi nasara da kuri’u masu rinjaye kan Farfesa Jerry wanda yakwan biyu da sauya sheka daga PDP zuwa SDP.*
*SDP dai tsohuwar jam’iyya ce a Najeriya da ta samo asali tun zamanin mulkin soja na Janar Babangida wacce ta kirkiro jam’iyyu biyu da su ka hada da SDP da NRC.*
*Ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul a Turkiyya ya ce sam ba gaskiya ba ne labarin wai a harabar ofishin sa a ka kashe dan jaridar nan na Saudiyya Jamal Khashoggi.*
*Jami’in na Saudiyya ya karyata labarin da kamfanin dillancin labarun REUTERS ya yada da ke cewa an kashe Kashoggi ne wanda ya bace a cikin ofishin jakadancin. Saudiyya za ta turo jami’an bincike na musamman zuwa Turkiyya don gano hakikanin abun da ya faru kan dan jaridar.*
*Shugaban Turkiyya Receb Tayyed Erdoan ya ce ya na bukatar sanin duk bayanai bayan bincike kan halin da Jamal Khashoggi ke ciki.*
*Ibrahim Baba Suleiman*
*Jibwis New Media*
*28-Muharran-1440*
*09-October-2018*

No comments