5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Gwamnatin Tarayya Ta Kammala Aikin Samar Da Katafaren Cibiyar Wutar Lantarki A Jihar Kano - Arew@Blog Gwamnatin Tarayya Ta Kammala Aikin Samar Da Katafaren Cibiyar Wutar Lantarki A Jihar Kano - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Gwamnatin Tarayya Ta Kammala Aikin Samar Da Katafaren Cibiyar Wutar Lantarki A Jihar Kano



Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi nasarar kammala aikin samar da cibiyar wutar lantarki mai karfin 30/40MVA 132/33kV' a garin Wudil dake jihar Kano.

A ziyarar gani da ido da cibiyar kafar yada labarai ta shugaba Buhari (The Buhari New Media Centre) ta kai wurin aikin a jiya Laraba karkashin jagorancin Hadimin Shugaban Kasa, Bashir Ahmad, wanda zai kara karfin wutar lantarki ga cibiyar samar da wuta ta jihar Kano, aikin zai fadada samar da wuta a kananan hukumomin Gaya, Takai, Garko Wudil da sauransu.

Wadannan garuruwa wadanda suna daga cikin kwastomomin cibiyar samar da wutar lantarki ta jihar Kano, ana sa ran za su samu karin wadatar wuta.

No comments

Powered by Blogger.