'Badakalar da aka tafka a zabukan fitar da gwani a Najeriya'
Zabukan fitar da gwani na jam'iyyu da aka gudanar a daukacin fadin Najeriya sun nuna cewa babu wani ci gaba a yanayin gudanar da siyasa a kasar tun bayan zabukan shekarar 2015.
Wadannan zabukan fitar da gwanin da aka zabi 'yan takarar da za su rike kanbun jam'iyyun a zaben shekara mai zuwa ya haifar da haniya da yamutsi a daukacin fadin kasar.
A wasu jihohi batun ba shi da banbanci da yaki.
Matsala ta farko da jam'iyyun suka samu ita ce, samun masu neman takara masu yawan gaske a jihohi da dama.
Ga misali a jihar Borno, mutane 25 ne suka biya naira miliyan 22 suka sayi fom din da zai ba su damar tsayawa takarar gwamna a jihar.
A jihohin Nasarawa da Imo da Kwara da kuma sauran jihohi kuwa, masu neman takarar na da yawan gaske.
Wannan ya sanya aka samu zabukan cikin gida cike da rudani da hayaniya, kuma ya zama lamari mai wahala ga jam'iyyun su tabbatar da bin dokar jam'iyya.
Wata matsalar ita ce yadda wasu masu neman takarar suka dauki zaben fitar da gwanin a matsayin babban zabe.
Ga misali, a yankunan da jam'iyyar APC ke da karfi, wasu 'yan takarar na ganin samun tikitin jam'iyyar tamkar nasara ce ga babban zaben, don haka suke yin bakin kokarin samun tikitin.
Kwatankwacin lamarin da ke a jam'iyyar PDP a jihohin da take da karfi, musamman a Kudu maso Gabashi da kudu maso Kudanci da kuma wasu jihohin arewaci da suka kunshi Taraba da Gombe.
A jihar Gombe, an fafata matuka a neman takarar kujerar gwamnan jihar inda 'yan daba da ke goyon bayan wani mai neman takara suka yi dirar mikiya a wurin zaben, suka kuma yi kaca-kaca da shi bayan sun lura cewa zaben ba ya yi wa dan takararsu yadda yake so.

Matsalolin da su ka dabaibaye zabukan
A wurare da dama, jami'an jam'iyyu sun mayar da ranaku da wuraren zaben da kuma sunayen wakilan jam'iyyun a zabukan tamkar wasan yara.
An tabbatar da faruwar wadannan a manyan jam'iyyun APC da PDP. Sai jami'an su sanar da ranar zabe, take kuma su sauya wurin bayan sun bayar da dalilai marasa gamsarwa.
A kan yi hakan ne domin rikita tunanin wasu masu neman takarar da ba su ake so ba, don amfanin masu neman takarar da suke kauna.
Wannan dambarwar game da ranakun zaben ta kai har karshen mako lokacin da Hukumar Zabe Mai Zaman kanta INEC ta sanya domin kammala zabukan fitar da gwani.
A wani batun kuma, jami'an jam'iyyun na sanya ranakun zaben amma ba za su sanar da masu neman takara wurin da za a gudanar da shi ba, ko kuma su sanar da wurin amma su sauya a kurarran lokaci.
Duk da haka, wasu mashahuran dabaru na manyan 'yan 'jam'iyya kamar gwamnoni wajen murde zaben shi ne na sauya sunayen wakilan ana tsakiyar gudanawar da zabe.
Har wa yau, wata mummunar hikima ita ce tattare wakilan a boye su a wani otal, wanda ba mai iya kai wa gare su don hana wasu masu neman takarar bayyana masu manufofinsu domin su zabe su.

Wani muhimmin lamari kuma shi ne yadda kudi ka taka muhimmiyar rawa a siyasar ta Najeriya.
Wakilan jam'iyyun na karbar kudi makudai ta kowace fuska daga masu neman takara.
Wannan ce ta sanya wasu masu neman takarar a jam'iyyar APC, suka bukaci a gudanar da zaben fitar da gwani na 'kai-tsaye', inda duk dan jam'iyya da ke da rijista zai kada kuri'a ya zabi mai neman takarar da yake so.
Sun yi amannar cewa wannan tsarin ya fi inganci wajen tabbatar da karbuwar mai neman takara, kana zai taka birki ga wakilai masu kwadayi



No comments