An Tashi Barambaran A Wurin Taron Ficewar Takai Daga Jam'iyyar PDP

A yayin taron da aka gudanar domin cimma matsaya game da jam'iyyar da dan takarar Gwamnan Kano na PDP Salihu Sagir Takai da wasu jiga-jigan PDP dake jihar Kano za su koma idan sun bar PDP, an samu bambancin ra'ayi, wanda hakan ya sa aka tashi taron ba tare da an fahimci juna ba.
Haka kuma a yayin taron wani da ya tashi yana 'sai Atiku Abubakar', wasu sun maida masa da martanin 'karye ne ba ma yi'.
Majiyarmu ta gano cewa Takai da sauran magoyan bayan nasa ba su da niyyar komawa APC domin ko ambaton APC ba a yi ba a wurin taron.
Shugabannin taron dai sun bukaci a ba su lokaci zuwa yammacin yau domin sanar da uwar jam'iyyar PDP sabuwar jam'iyyar da Takan zai koma.
Daga cikin jam'iyyun da ake sa ran Takai da sauran jiga-jigan PDPin na Kano za su koma, sun hada da PRP, ADC, GPN da sauransu.

No comments