5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Rahama Sadau Ta Sake Samun Lambar Yabo - Arew@Blog Rahama Sadau Ta Sake Samun Lambar Yabo - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Rahama Sadau Ta Sake Samun Lambar Yabo

Har yanzu tauraron fitacciyar jaruma Rahama Sadau na cigaba da haskawa inda ya samu wani sabon lambar yabo a karshen makon da ya shude.


Jarumar ta samu kyautar jaruma mai bada taimako wajen haddasa zaman lafiya  a bikin Peace Achievers Awards 2018 wanda aka gudanar ranar Asabar 22 ga watan Satumba a dakin taro na Transcorp hilton Hotel dake Abuja.
Rahama ta nuna farin cikin ta samun wannnan kyautar a shafin ta na kafafen sada zumunta.

Gasar Peace Achievers Awards biki ne wanda aka gudanar a ko wani shekara domin karrama fitattun hukumomi da yan kasar dake taka rawar gani wajen raya zaman lafiya a kasar.

Bikin gasar na bana shine karo na bakwai.
Kyautar da jarumar ta samu shine na uku da zata samu bana bayan na jaridar Leadership da gidauniyar Global Women Empowerment network

No comments

Powered by Blogger.