An Gano Motar Tsohon Manjo Janar Alkali A Filato
An Gano Motar Tsohon Manjo Janar Alkali A Filato
___¥__
*
Kwamitin da Shugaban Rundunar Sojan kasa, Tukur Burutai ya kafa da ya kunshi ‘yan sanda, jami’an kashe gobara sun gano motar Manjo Janar IM Alkali ( Mai Ritaya) da aka daina jin duriyarsa tun 3 ga Satumba, 2018.

An gano motar ne yau a wani kududdufi da ke yankin Gundumar Lafendeg Du a Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.
Yau kimanin mako guda ke nan da Rundunar sojojin Najeriya take janye ruwan kududdufin da zummar gano motar bayan bayanan sirrin da ta samu na cewa an jefa motar Manjo Janar Alkali a ciki.
Amma yaya maganar gawarsa sannan kuma su wa suka kashe shi?
No comments