5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Yacce ake SUYA (TSIRE) - Arew@Blog Yacce ake SUYA (TSIRE) - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Yacce ake SUYA (TSIRE)

INGREDIENTS:
Nama, borkono, kuli-kuli, citta, kimba, kanunfari, masoro, thyme, curry, busashen tafarnuwa da sauran spices. Mangyada, gishiri, maggi sai tsinkin tsire.

PROCEDURE: Ki daka dukkanin spices naki tare da kuli, amma kulin ya ďan fi yawa, kuma ki sanya maggi da gishiri. A zabi nama mai kyau wanda babu kitse sosai a jiki, sai ki yanka shi sirara ta kwance da dan tsayi kadan sai ki ďauko tsinken tseren ki jera wannan naman a jiki. Wato in kin huda ta ciki sai ki fitar da shi ta waje.
Daga nan sai ki sami kwano ki zuba mangyada dai-dai misali tare da gishiri da maggi kaďan ki shafe jikin naman duka. Kina yi kina sanya shi cikin haďin kulin ya kama jikinsa da kyau. Daga nan in a oven ne sai ki yi ta jera su suna gasuwa. In ma a rushi ne duka ba damuwa.
Tsire fa shine amarya tashi watssake
Idan an je siya a rinka hana su sanyawa cikin newspaper domin yana da rubutu a jikinsa. Kuma wasu likitoci sun ce yana haddasa ciwon kidney (qoda) Allah Ya kare mu.

No comments

Powered by Blogger.