Sojojin Najeriya sun yi bore a Maiduguri
An shiga wani tashin hankali a filin jigin saman birnin Maiduguri inda rahotanni suka ce Sojoji sun ta yin harbi sama domin nuna rashin amincewa da matakin dauke su daga Maiduguri a jihar Borno.
Sojojin sun ki shiga jirgin da zai kwashe su daga Maiduguri zuwa karamar hukumar Marte da ke kan iyaka da Nijar.
Bayanai sun ce sojojin da ke fada da kungiyar Boko Haram sun shafe kusan sa'o'I hudu suna harbi sama tare da yin barazana ga kwamandojinsu.
Lamarin ya faru ne da yammacin lahadi kuma rahotanni sun ce kura ta lafa sai dai kuma babu tabbacin ko sojojin sun tafi Marte inda aka bukaci su koma.
Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato wasu daga cikin sojojin na cewa fushi ne dalilin da ya sa suke harbi, suna cewa ga dalilin da zai sa a dauke su zuwa wani wuri ba bayan sun yi shekaru hudu a Maiduguri.
Babu dai wata sanarwa daga rundunar sojin Najeriya ko kuma rundanar da ke yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar game da boren na jami'an sojin.
No comments