5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Cutar Kwalara ta barke a Jamhuriyar Nijar - Arew@Blog Cutar Kwalara ta barke a Jamhuriyar Nijar - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Cutar Kwalara ta barke a Jamhuriyar Nijar

Cikin wadanda suka kamu da cutar amai da gudawar kananan yara sun fi shan wahala
Cutar amai da gudawa da ta barke a Jamhuriyyar Nijar ta hallaka kusan mutane 19.
Mutane dubu 1,168 ne suka kamu da cutar a gundumar Madarunfa ta jahar Maradi da ke yankin kudancin kasar.
Sama da wata daya ke nan da aka samu barkewar wannan cuta a wannan yanki, kuma cikin wadanda cutar ta shafa yara kanana sun fi yawa.
Dr Alhaji Ibrahim Tasiu shi ne darakatan kiwon lafiya a gundumar ta Madarunfa kuma ya shaidawa BBC cewa daga ranar Juma'ar da ta gabata zuwa yanzu kusan mutane 19 suka mutu.
Mutanen da suka kamu da wannan cuta ta amai da gudawa na kwance a babban asibitin birnin Maradi ne, kamar yadda hukumar jin kai ta Majalasar Dinkin Duniya wato OCHA ta sanar.
Rahotanni sun bayyana cewa a garin N'Yelwa ne aka fara samun mutum na farko da ya kamu da cutar tun a farkon watan Yuli da ya wuce.
Sai dai ministan ma'aikatar lafiya Nijar Illiassou Mai Nassara ya shaidawa manema labarai cewa, tuni gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin dakile yaduwar cutar zuwa wasu sassan kasar musamman yankunan karkara.
Kungiyar likitocin kasa da kasa Medecin Sans Frontiere, da Asusun kula da yara na Majalasar Dinkin Duniya sun isa yankin da cutar ta bulla don taimakawa wadanda suka kamu da cutar.
Sannan za su yi aikin wayar da kan al'umma kan muhimmancin tsaftar muhalli da wanke hannu kafin ci da bayan kammala cin abinci da tsaftar kayan abincin musamman kayan lambu da 'ya'yan itatuwa.

No comments

Powered by Blogger.