Higuain Ya Koma Ac Millan Daga Juventus A Matsayin Aro
Dan wasa gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Gonzalo Higuain, dan kasar Argentina ya koma kungiyar kwallon kafa ta AC Millan dake kasar Italiya a matsayin aro na shekara daya bayan kungiyoyin biyu sun amince da yarjejeniyar. Dan wasan, mai shekara 30 a duniya ya koma Jubentus ne daga kungiyar Napoli shekaru uku da suka gabata kuma ya taimakawa kungiyar Juventus wajen lashe kofin siriya A da kuma wasan karshe na cin kofi zakarun turai da Real Madrid ta doke su. Tun frako dai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ce take son siyan dan wasan wanda suka taba aiki tare da kociyan kungiyar na yanzu, Mauricio Sarri a kungiyar Napoli sai dai bisa dukkanin alamu AC Milan ta doke Chelsea wajen samun dan wasan. Har ila yau AC Millan tanada damar siyan dan wasan a kakar wasa mai zuwa akan kudi fam miliyan 32 idan har dan wasan ya buga abinda ya kamata a kungiyar kuma acikin cinikin da akayi dan wasa Leonardo Bonucci zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Jubentus bayan ya koma AC Millan a kakar wasan data gabata. A yau ne dai ake saran za a gwada lafiyar dan wasan a kungiyar kwallon kafa ta AC Millan bayan an kammala cike ciken takardu tsakanin kungiyoyin biyu da kuma wakilin dan wasan kuma dan uwansa na jinni. Higuain dai ya taba bugawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wasa a shekarun baya kuma ya wakilci kasarsa ta Argentina a gasar cin kofin duniyar da aka kammala a kasar Rasha inda kasar Faransa ta doke su daci 4-3 a wasan falan
No comments