Fim Din ‘In Search Of The King’ Ya Samu Goyon Bayan Masarautar Ringim
A farkon watan nan na Yuli aka shiga aikin wani fim na turanci mai suna In Serach of the King, wanda yake ba da tarihi da yanayin masarautar Kasar Hausa tun tsawon shekaru masu yawa da suka gabata. Duk da cewar fim ne da aka yi shi da harshen turanci amma idan ka dauke yaren na turanci da aka yi amfani da shi, to duk wani abu da aka nuna a fim din yana nuna ydda tsarin rayuwar masarautar kasar Hausa take ta fannin al’adu, ilimi, mulki da mu’amalarsu ta yau da gobe. Wani abin birgewa game da wannan fim din kusan za a iya cewa shi ne fim na farko da aka nuna yadda Sarautar kasar Hausa take a zahiri, ba wai kwaikwayo ba. Domin kuwa an yi amfani da gadon sarautar Ringim ne inda Sarkin na Ringim dake jihar JIgawa ya amince a yi aikin fim din a masarautarsa kuma ya bayar da aron duk wata fada da ake bukata domin gudanar da ikin fim din. Kuma ya ba da mutanesa da suka rinka kula da aikin don su tabbatar an bi tsarin sarautar ba tare da an yi mata kutse ba, kamar yadda aka saba yi a sauran finafinan da ake yi a Kannywood. Fim din dai labarin masarautu ne masu karfi har guda uku a kasar Hausa kuma Ali Nuhu da Yakubu Muhammad da Abba Almustapha suka fito a matsayin sarakuna. Sai Nafisa Abdullahi da ta fito a matsayin Gombiya kuma jarumi mai tasowa Abdullah Amdaz ya fito a matsayin Yarima. Kabiru Musa Jammaje shi ne ya dauki nauyin shiryawa. Ganin yadda fim din ya samu amincewa ga masauratar Ringim har aka yi aikin a cikin fadar, mun tambayi jagoran shirin Malam Kabiru Jammaje a game da matakan da suka bi har suka samu amincewar masarautar da kuma yadda aikin ya gudana. Inda ya shaida mana cewar, “Tun da farko ma dai da muke yin aiki a kan rubuta labarin, gaskiya ba mu dauka za mu je har Ringim domin yin aikin ba, saboda a tunaninmu za mu samu wajen da za mu yi aikin a kusa, sai ya zama mun je gurare da dama amma sai muka ga bai yi mana yadda muke so ba, don haka sai aka kawo shawarar a tafi wajen Sarki Ringim za a iya samu. Don haka da muka je muka yi gaisuwa kuma sai muka ba da takardar neman izini ta a ba mu dama mu yi amfani fa masarautar don gudanar da aikin, kuma abin farin ciki suka nuna goyon baya suka aiko mana da takardar amincewa ta hannun Danmajen Ringim. Kuma wani abu a ya zo mana bazata wanda ya kara inganta mana aikin shi ne yadda masarautar ta ba mu mai kula da mu ya kasance tare da mu wato Yariman Ringim. Don sun ce suna kallon finafinai da ake yi na sarauta, amma ba a nuna masarautu yadda ya kamata, don haka tun da a masarautarsu za a yi ba za su zuba ido su ga an murguda yadda tsarin masarauta yake ba, don haka ba biyan su muka yi ba sune suka ga dacewar yin hakan, don suna daukar cewar wani nauyi ne a kansu musamman da muka nuna musu cewa fim din za a yi shi da turanci ne kuma zai shiga kasashen Turai da ma wasu nahiyoyi na duniya, don haka suka ga hakkinsu ne su tsaya su tabbatar an yi tsarin sarautar da ta shafi Arewacin Najeriya yadda ya kamata. Kuma na gamsu sosai da tsayawar tasu domin kuwa da an bar mu da kanmu da mun yi kurakurai. Saboda hatta yadda Sarki yake zama da kafar da zai kada da yanayin yadda yake magana da saka kaya duk sai da suka nuna mana don ko rawani ma sune suka daura wa Sarki da Galadima da Waziri da Shamaki, don kowa da yanayin yadda yake rawaninsa. Don shi da kansa Yariman wato dan Sarkin ya ce fim din duk wanda ya kalle shi in dai ya san tsarin sarautar to ya san an bi tsarin yadda ake gudanar da ita. Don sarauta aka nuna ta sosai ba ta wasan kwaikwayo ba, kuma gaskiya an samu canji sosai. Ya ci gaba da cewa, “Duk fim din ya kunshi masarautu ne guda uku masarautar Tumashe wadda Sarkinta shi ne Abba Almustapha, sai masarautar Gwani da wadda Yakubu Muhammad ne Sarki sai masarautar Salbana da Alinu Nuhu ya zamo Sarki. Kuma a yanzu mun fara ne da masarautar Salbana a garin Ringim, yanzu abin da ya rage mana sune sauran masaautu guda biyu ta Gwarida da kuma ta Kumashe. Saidai su ba a garin Ringum din za a yu su ba, za a yi su ne a garin Kano da kuma Danbatta.”
Sai dai ganin yadda Masarautar Salbana ta samu kulawa daga masarautar Ringim, kasancewar sauran masarautun ba a can za a yi su ba, ko su ma za su samu kulawa daga masarautar? Sai Jammaje ya ce, “Lallai mun yi magana da Yariman kuma ya tabbatar mana cewar duk da ba a garinsu ba ne zai zo da kansa a yi komai a gabansa. Don haka muna godiya a gare shi da kuma masarautar Ringim bisa gudunmawar da suka ba mu.”
Shi ma Daraktan fim din Balarabe Murtala Baharu ya shaida mana cewar, “Ni abin da zance na amfana da shi a fim din In Search of the King duk fim na duniya idan za a yi ana karuwa da Darakta ne daga irin yadda yake gudanar da aikinsa, amma a wannan fim din ni na kara ilimi saboda irin abin da aka zo da shi na nuna ka’idar yadda sarauta take zaman fada, mu’amala, maganganu, sanya tufafi da yadda ake zama. Ni a rayuwata ban taba tunanin haka fada ake ba, don haka a matsayina na mai ba da umarni na karu sosai kuma kalubalen da na fuskanta ban taba yin aiki ina tare da masu ba da umarni har guda hudu ba sai a In Search of the King. Wanda yake kula kalmomin da ake firtawa daban, wanda yake kula da kayan da ake sakawa daban, wanda yake lura da zaman da ake yi daban. Sannan wadanda suke kula da aikin da ni kaina nake yi daban. Don haka wannan fim din ya zama zakaran gwajin dafi. Kuma abin da ya fi saka ni farin ciki da shi mai fim din ya ce shi a shirye yake da ya sake linka wani kudin da ya yi wa fim din kasafi domin a samu aiki mai inganci don bin diddigin da ake yi wa fim cin bai sa shi ya karaya ba, kuma ya yarda fim din da aka ce za a yi sati biyu, ya amince ya kai sati 4 ma ana yin aikinsa. Don haka wannan ba karamar nasara ba ce. Kuma daman abin da muka rasa a cikin finafinanmu kenan shi ya sa za ka ga ana samun kurakurai, domin ka ga a cikin wannan aikin namu akwai rana guda da ta zamo sin daya kawai muka dauka saboda bin tsari na ya kamata a dauke shi daidai yadda mai kallo zai dauke shi ya kalle shi a matsayin gaske ne ake yi shi ba wasa ba.” Nafisa Abdullahi ita ce jarumar da ta fito a matsayin Gimbiya a fim din, ta bayyana cewa, “Duk da cewar wannan fim din ba shi ne na farko da nake fitowa a cikin sarauta ba, to shi wannan ya zo mini da siffa ta daban, kasancewar sa na Turanci. Don haka a nan zan iya cewa In Search of the King ya bambanta da sauran finafinan da na saba fitowa, kuma aikin ya burge ni sosai don na ji dadinsa.” Shi ma jarumin fim din Abdullahi Amdaz wanda ya kasance fim din ne na farko a gare shi da ya zamo babban jarumi, ya shaida mana cewar, “Na yi farin cikin kasancewa a matsayin jarumin wannan fim din, “Duk da cewa shi ne fim na farko da na zamo babban jarumi a cikinsa. Don haka sai na ji a zuciyata zan yi kokari na yi duk wani abu da zai ba da fa’ida kuma ya fito da kima da darajar aikin. Na fito a matsayin Bello da ya ke yawo a tsakanin masarautu guda uku domin neman cimma wani burina kuma a hakan na samu kaina a yanayi kala-kala don na samu na yi.” Zuwa yanzu dai an kammala kashin farko cikin kashi uku na fim din har an tafi hutu, sai a watan Oktoba za a ci gaba da kashi na biyar da na uku a garin Kano da kuma Danbatta. Fim din dai ya kunshi jarumai masu yawan gaske da suke aiki a cikin fitattun ‘yan Kannywood akwai Ali Nuhu, Abba Almustapha, Yakubu Muhammad, Nafisa Abdullahi, Rabi’u Rikadawa, Rukayya Dawayya, Shehu Hassan Kano, Shu’aibu Yawale, Tijjani Faraga da sauransu.

No comments