Abin da na fada wa Atiku Abubakar a Kaduna – Dr Ahmad Gumi
Mun samu dubban ra'ayoyin jama'a bayan wallafa wani hoto da ke nuna fitaccen malamin addinin Musuluncin nan a Najeriya Dokta Ahmad Gumi tare da tsohon Mataimakin Shugaban kasar Atiku Abubakar a wurin wani daurin aure a Kaduna ranar Juma'a.
Dokta Gumi ya dade yana sukar wadansu manufofin gwamnati Shugaban kasar Muhammadu Buhari musamman lokacin tafsirinsa na azumin watan Ramadan na bana.
Atiku Abubakar, wanda ya koma jam'iyyar PDP a karshen bara, yana cikin wadanda suke neman shugaban kasar a zaben 2019.
Wannan ya sa muka tuntubi malamin ta waya, inda muka tambaye shi abin da ya fada wa Atikun lokacin da suka hadu a Kaduna.
"Bayan da muka yi gaishe-gaishe, na yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar bayanin cewa akwai wani daurin aure da muka hadu da ni da shi, aka dauki hotonmu da ni da shi da wani tsohon gwamna," in ji Dokta Gumi.
"Sai nake ba shi labarin mutane sun ce tun da an gan mu tare da ni da shi tare da wancan tsohon gwamnan, to na zama dan PDP. Al hali lokacin shi kansa dan APC ne."
Ya ce hakan yana nuna cewa "duk lokacin da aka gan shi da wani dan siyasa" sai wadansu mutane su rika yi musu mugun zato.
- Za ku iya sauraron cikakkiyar tattaunawar da muka yi da Dokta Gumi kan batun, idan kuka latsa alamar lasifika da ke sama.
Har ila yau Dokta Gumi ya ce abu na uku da ya fada masa shi ne shi ba dan kowace jam'iyya ba ne, "ba na PDP, ba na APC."
Sai dai ya ce su ba za su iya yin shuru "idan muka ga za a cuci jama'a ko kuma za a taba addininmu ba."
Ga sauran wadansu ra'ayoyin jama'a game da hoton - kuma za ku iya bayyana naku ra'ayoyin a shafin namu na Facebook:
No comments