5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Sunayen ‘yan ta’addan da ‘yan sanda ke zargin Bukola Saraki da daukan nauyin ayyukan su - Arew@Blog Sunayen ‘yan ta’addan da ‘yan sanda ke zargin Bukola Saraki da daukan nauyin ayyukan su - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Sunayen ‘yan ta’addan da ‘yan sanda ke zargin Bukola Saraki da daukan nauyin ayyukan su

Sunayen ‘yan ta’addan da ‘yan sanda ke zargin Bukola Saraki da daukan nauyin ayyukan su

A yau ne hukumar ‘yan sanda ta aike da takardar gayyata ga shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, bayan wasu gungun ‘yan fashi da aka kama sun bayyana cewar Saraki na daga cikin mutanen da suke yiwa ayyukan ta’addanci.

Hukumar ta ‘yan sanda tace yanzu haka tana tsare da mutane 22 da take zargi da hannu cikin fashin bankunan garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu tare da kashe mutane kimanin mutumin 33.

Ga jerin sunayen mutanen da inda suka fito kamar yadda hukumar ‘yan sanda ta wallafa

Sugabannin gungun 'yan fashin shine:
1. Ayoade Akinnibosun,mai shekaru 37 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State.

2. Ibukunle Ogunleye, shekaru 36 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State. Ya kashe mutane 2

3. Adeola Abraham, shekaru 35 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State. Ya kashe mutane 5

4. Salawudeen Azeez, shekaru 49 – daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State. Ya kashe mutane 2

5. Niyi Ogundiran, shekaru 37 –daga Oro, Irepodun LGA, Kwara State.
Ya kashe mutane 2

6. Michael Adikwu,shekaru 30 – Ya kashe mutane 22, yawancin su 'yan sanda.

7. Kabiru Afolabi, shekaru 26

8. Omoseni Kassim, shekaru 28

9. Kayode Opadokun, shekaru 35

10. Kazeem Abdulrasheed, shekaru 36

11. Azeez Abdullahi, shekaru’ 27

12. Adewale Popoola, shekaru 22

13. Adetoyese Muftau, shekaru 23

14. Alexander Reuben, shekaru 39

15. Richard Buba Terry, shekaru 23

16. Peter Jasper Kuunfa, shekaru 23

17. Ikechukwu Ebuka Nnaji shekaru 29

18. Moses Godwin, shekaru 28

19. Adeola omiyale, shekaru 38, daga garin Isanlu Isin, Isin LGA, Kwara State.

20. Femi Idowu, shekaru 34

21. Alabi Olalekan, shekaru 49-mai taimakawa gwamnan jihar Kwara na musamman

22. Yusuf Abdulwahab, shekaru 58 –Shugaban ma'aikatan jihar Kwara.

No comments

Powered by Blogger.