Zan sa kafar wando daya da masu boye fetur — Buhari
Farashin mai daga 'yan bumburrutu na da tsada sosaiShugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce shi zai yi maganin wadanda suka haddasa tsadar man fetur a fadin kasar.
Shugaban ya dauki alwashin yin haka ne a wani jawabin da ya yi wa 'yan kasar na sabuwar shekarar 2018.
Shugaba Buhari ya nuna bakincikinsa kan wahalar da 'yan Najeriya suka shiga a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara saboda tsadar man fetur wadda ya ce wasu 'yan Najeriya ne suka haddasa ta.
Ya ce shi ba zai lamunci irin wahalar da 'yan Najeriya suka sha ba a lokacin bukukuwan duk da matakan da kamfanin man fetur na kasar (NNPC) ya dauka na samar da mai a wuraren ajiyan mai.
Shugaba Buhari ya lashi takwabin gano musabbabin yi wa 'yan Najeriya gabadaya abin da ya kira ci-da-ceto.
Ya kara da cewar shi zai hana ko wacce kungiya da ta haddasa matsalar damar iya sake haddasa ta.
A karshen shekarar da ta gabata ne dai Najeriya ta fara fuskantar tsadar man inda babu mai a mafi yawan gidajen mai kuma masu sayar mai din suke sayar wa kan farashin da ya dara naira 145 da gwamnati ta amince da shi.
Wannan ya janyo ce-ce-kuce tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar dillalan man fetur ta kasar.
Wasu rahotanni sun ce an samu tsadar man ne saboda tsadar danyen mai a kasuwar duniya wadda ta sa kudin man fetur ya zama naira 171 kan ko wane lita, yayin da kudin da gwamnatin kasar ta amince a sayar da mai bai wuce naira 145 ba.
Tsadar mai ka iya sa tsadar rayuwa ta ta'azzara
No comments