5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Karanta yadda ake 'cin zarafin matan Nigeria a Facebook' - Arew@Blog Karanta yadda ake 'cin zarafin matan Nigeria a Facebook' - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Karanta yadda ake 'cin zarafin matan Nigeria a Facebook'


Shugaban Facebook, Marck Zukerberg ya ziyarci fadar shugaban da ya ziyarci Najeriya kwanakin baya
Wani bincike ya nuna cewa mata da dama a arewacin Najeriya su na kaurace wa intanet sakamakon barazana da cin zarafin da suke fuskanta daga ma'abota shafukan sada zumunta, musamman ma Facebook.
Kungiyoyin da ke fafutikar kare hakkin jinsi na kallon lamarin a matsayin wani nau'i na tauye 'yancin mata, wanda ke bukatar mahukunta su dauki matakan yaki da shi.
Wannan lamari ne ya sa Cibiyar Sasahar Sadarwa da ci gaban al'umma da ke Kano ta shirya wani taro don nazarin rahoton tare da duba hanyoyin magance matsalar.

Kungiyoyin da ke fafutikar kare hakkin jinsi na kallon lamarin a matsayin wani nau'i na tauye 'yancin mata
Ibrahim Isa ya tattauna da Mallam Muhammad Awwal Garba daga hukumar Hisbah ta jihar Kano da Maryam Ado Haruna, jami'a a wannan cibiya ta fasahar sadarwa da aka fi sani da CITAD, inda suka yi masa bayanin yadda girman matsalar take.
Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa domin sauraron cikakkiyar hirar tasu:


No comments

Powered by Blogger.