Karanta yadda ake 'cin zarafin matan Nigeria a Facebook'
Wani bincike ya
nuna cewa mata da dama a arewacin Najeriya su na kaurace wa intanet
sakamakon barazana da cin zarafin da suke fuskanta daga ma'abota
shafukan sada zumunta, musamman ma Facebook.
Kungiyoyin da ke
fafutikar kare hakkin jinsi na kallon lamarin a matsayin wani nau'i na
tauye 'yancin mata, wanda ke bukatar mahukunta su dauki matakan yaki da
shi. Wannan lamari ne ya sa Cibiyar Sasahar Sadarwa da ci gaban al'umma da ke Kano ta shirya wani taro don nazarin rahoton tare da duba hanyoyin magance matsalar.
Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa domin sauraron cikakkiyar hirar tasu:
No comments