Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa masu gudun hijira su kimanin 35,000 da suka kwarara cikin kasar Kamaru, su nan nan lafiya a cikin kasar.
Wannan adadin masu gudun hijira sun tsere ne daga garin Rann.
Sun tsere ne cikin makonni biyu na karashen watan Janairu, a dalilin barazanar mummunan hare-hare da Boko Haram suka rika kai wa garin kwanan nan.
Cikin 2017 jirgin sojojin Najeriya ya jefa bam a bisa kuskure, a kan mazauna sansanin gudun hijira a ran.
Cikin watan Janairu kuma an kai wa garin na Rann hari har sau biyu.
Hukumar ta tabbatar da cewa babu wata barazana a kan masu gudun hijirar, tun bayan yunkurin da mahukuntan kasar suka yi na koro su zuwa gida Najeriya.
A nan Najeriya, akwai dimbin masu gudun hijira daga Jamhuriyar Kamaru, masu yawan gaske.
Babban Jami’in Hukumar da ke Kamaru, Allega Baroccha, ya ga akwai tsoron maida su Najeriya sosai a zukatan masu gudun hijira daga Najeriya.