5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Muhawarar jihar Kano: Abubuwa 7 da ba za a yi mantawa da su ba - Arew@Blog Muhawarar jihar Kano: Abubuwa 7 da ba za a yi mantawa da su ba - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Muhawarar jihar Kano: Abubuwa 7 da ba za a yi mantawa da su ba

Ibrahim Isah
A jerin muhawarar da sashen Hausa na BBC ke gudanarwa a wasu daga cikin jihohin Najeriya, a ranar Asabar ne aka gudanar da muhawarar 'yan takarar gwamna a jihar Kano.
'Yan takarar da suka hallarci muhawarar sun hada da Mustapha Getso na jam'iyyar NPM, da Salihu Sagir Takai na jam'iyyar PRP da Maimuna Muhammad ta jam'iyyar UPP da Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP.
Sai dai dan takarar jam'iyya mai mulki ta APC a jihar, Abdullah Umar Ganduje bai hallarci zauren muhawarar ba.
'Yan takarar sun fadi abubuwa da dama da za su kawo ci gaba a jihar tasu ta Kano.
Mun yi waiwaye game da manyan abubuwa bakwai muhimmai game da muhawarar wadanda da wuya a manta da su:

1. Rashin zuwan Ganduje

Kin halartar dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC Abdullahi Ganduje yana daya daga cikin abin da ba za a yi mantawa da shi ba a wannan muhawarar.
Musamman ganin yadda aka rika dakon zuwansa daga farkon fara muhawarar har aka kai karshe bai halarta ba.
Sai dai a wata sanarwa da kwamitin yakin neman zaben gwamnan ya fitar, kwamitin ya ce bai samu halartar muhawarar ba ne saboda ta ci karo da yakin neman zaben gwamnan da aka tsara tun tuni.

2. Zan kawo tsarin iyali - Mustapha Getso

Mustapha Getso na jam'iyyar NPM ya ce zai kawo tsarin iyali idan ya zama gwamna a yunkurinsa na magance matsalar almajiranci. Ya ce zai wayar da kan iyaye su daina haihuwar 'ya'ya rakwacam suna tura su bara.
Ya sha alwashin bunkasa kananan sana'o'i irinsu kafinta da walda da gini.
                      Advertisement


                            MUSTAPHA GETSO

3. Kwankwaso ba zai sa na yi abin da ba daidai ba - Abba

Dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ya ce ya tabbatar tsohon gwamnan jihar Rabi'u Musa Kwankwaso ba zai sa ya yi abin da ba daidai ba.
Da aka tambaye shi, shin idan Kwankwaso ya bukaci ya yi abin da ya saba da manufofin ci gaban Kano zai bijire masa, sai ya ce ba bijire masa zai yi ba, zai yi kokarin ganar da shi gaskiya ne ta hanyar bayani.
Ya ce, "Na san halin Kwankwaso tamkar yadda na san yunwar cikina; ina da tabbaci ba zai sa na yi abin da ya sha bamban da ci gaban Kano ba."
              
ABBA KABIR YUSIF

4. Mata ne ke mulkin gwamnonin Kano - Maimuna Muhammad

'Yar takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar UPP, Hajiya Maimuna Muhammad ta bayyana cewa mata ne ke jan ragamar mulkin jihar.
"Mata mu ke daukar ciki, muyi reno, mulki ba zai gagari mace ba a jihar Kano" a cewar ta.
Sai ta kara da cewa " Su kansu mazan ba suke mulki ba a jihar kano, matan ne suke mulki"
Bayan da ta fadi hakan ne dakin taron ya kaure da dariya da sowa.
                            MAIMUNA MUHAMMAD
 5 . Zan magance matsalar daba - Takai
Salihu Sagir Takai, dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PRP, ya ce zai magance dabanci da inganta ilimi cikin kwana 100 zai gyara makarantun firamare da sakandare.
Zai yi amfani da kudin kananan hukumomi wajen inganta ilimi a mataki na farko.
Zai bayar da horo ga malamai da samar da kayan karatu.             
                          SALIHU SAGIR TAKAI
6. Masu bukata ta musamman sun halarci muhawara
Masu bukata ta musamman sun hallarci wannan muhawara, ciki har da makafi da guragu. 'Yan takarar gwamnan sun yi musu alkawuran inganta rayuwarsu.

7. 'Beraye sun yi yawa ba sa tsoron maguna'

A jawabinta na karshe 'yar takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar UPP, Hajiya Maimuna ta ce jam'iiyarta ba bakuwa ba ce, "saboda a da an santa. mai alamar damisa."
"Saboda beraye sun yi yawa kuma ba sa tsoron maguna. Shi ya sa muka dauko damara muka dauko wannan jam'iyya mai alamar domin mu hada yi maganinsu."
Daga nan ta yi fatan a yi zaben cikin lafiya da lumana.

No comments

Powered by Blogger.