Kwana 11: Yadda zaben Najeriya zai shafi kasar Ghana
Nan da kwana 11 ne za a gudanar da zabe a Najeriya, kasar da ta fi kowacce a nahiyar Afirka yawan al'umma da karfin tattalin arziki kuma mai fada a ji a nahiyar.
Ko ta yaya zaben da za a yi kasar zai shafi sauran kasashen Afirka kamar su Ghana? BBC Hausa ta yi bincike a kai.
Shehu Sani mai shekaru 30 da 'yan kai, yana da wani karamin shago a unguwar Sabon Zango da ke birnin Accra, dan kasuwa ne a kasar Ghana da ke sayar da kayayyakin Najeriya, inda kuma ya nuna damuwarsa a kan zaben kasar mai tafe.
Akwai huldar kasuwanci mai karfi tsakanin Najeriya da Ghana, inda ta ke yi wa kasar Ghana safarar iskar gas.
Haka kuma, akwai bankunan Najeriya da yawa a Ghana, wannan wata muhimmayar hanya ce ta sanya hannun jari a kasar ta Ghana.
Mr Vladimir Antwi wani masanin huldar kasa da kasa ne kuma ya yi wa BBC Hausa bayani a kan abinda ya sa zaben da za a yi a Najeriya zai shafi Ghana da ma sauran kasashen nahiyar Afirka baki daya.
Vladmir ya ce ''Akwai 'yan Ghana da yawa a Najeriya haka kuma akwai 'yan Najeriya da yawa a Ghana, Allah ya kiyaye idan wani tashin hankali ya faru a Najeriya, 'yan Najeriya za su tuttudo zuwa Ghana, don ba za su tsaya a Benin ko Togo ba, don haka, dole ne mu damu a kan abin da zai faru a zaben Najeriya."
Ya kuma ci gaba da cewa ''da yawa na tunanin matsalar Boko haram ce babbar matsala, watakila za su iya gudanar zabe a wasu sassan kasar."
''Amma a ganina babbar barazana ita ce tsarin mulki na Najeriya, da rashawa wanda zai iya mamaye zaben, wannan matsalar ce mafi girma a kan ta Boko Haram."
Hakazalika wasu al'ummar Ghana da BBC ta tattaro ra'yoyin su na ci gaba da bayyana fargabar su a kan zaben.
Wani mutum ya bayyana cewa "yana da muhimmanci mu san abinda yake faruwa a can saboda 'yan Najeriya da yawa sun zo nan neman kudi."
"Idan an yi zaben lami lafiya zasu iya komawa gida, amma idan aka samu rikici da yawan su zan su kara shigowa nan su dora mana nauyi."
Kananan 'yan kasuwa kamar su da dama nahiyar Afirka ta yamma baki daya za su zura idanu a kan zaben Najeriya da za a yi ran 14 ga watan Fabrairu tare da fatan ayi shi lamin lafiya.
No comments