Ko kun san dalilin da ya sanya matan Arewa suke auren 'yan kudu a yanzu?
Yan matan Arewa da yawa na auren samarin kudancin Najeriya, wani abu wanda ya zama salo a halin yanzu da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar.
Fiye da shekara 100 tun bayan da Turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka hada arewaci da kudancin Najeriya, ba a taba samun wani lokaci da ake samun auratayya tsakanin kabilun kasar ba kamar yanzu.
Mun samu zantawa da Hadiza Usman Yaro da Maryam Ladan, wasu mata biyu daga Arewa da ke auren 'yan kudu domin mu ji daga gare su.
"Mun hadu a wajen bikin kawata ne inda aka gaya mini cewa yana so na. Na ce me zai hada Hadiza da Mobolagi" a cewar Hadiza.
Hadiza ta bayyana mana cewa ba ta ba shi wani muhimmanci ba, saboda ta san yadda sha'anin auren wani kabila yake a kudu.
Hadiza ta bayyana soyayya da shaukin juna ya kama su, inda har ya kai su ga aure da samun zuriya a halin yanzu.
Ita Maryam a bangare daya, ta bayyana cewa sun hadu a jami'a ne a Malaysia.
Ta nemi taimako ne daga wajensa, inda daga baya soyayya ta mamaye zuciyoyinsu.
"Tun bayan da muka hadu sai nace wa kaina, ke wannan Bayarabe ne, me zai hada ki da shi?" a cewar Maryam.
Kalubalen da suka fuskanta kafin aure
A cewar Maryam, bayan da ta kammala karatunta ta dawo gida Najeriya, ta fada masu ga abin da ake ciki "amma mahaifina ya ce kwata-kwata bai yarda ba."
"Yan'uwana da mahaifiyata duka suna goyon bayana, mahaifina ne kawai bai yarda ba daga farko" a cewarta.
Maryam ta bayyana cewa hakan kwata-kwata bai girgiza Sahed ba.
Har ma yake ce mata ta yi wa iyayenta biyayya, "idan Allah ya kaddara aurensu, to za a yi."
Shi ma mahaifinsa bai yarda ba daga fari, amma mahaifiyarsa na goyon bayan abin a cewar Maryam.
Daga baya Allah ya yi ikonsa ga shi yanzu suna matsayin mata da miji.
Hadiza Yaro kamar Maryam, da ta bayyana soyayyarta sai mahaifiyarta ta shawarce ta "da ta bar zancen don ba abu ne mai yiyuwa ba."
Amma ita ta samu goyon bayan mahaifinta. "Mahaifina ya ce tun da ba ita ta ce tana so ba ai shi ke nan. Idan an aura mata ai ita za ta zauna da shi."
Shin mazan kudu Yarabawa sun fi na Arewa Hausa iya rikon mata ke nan?
A cewar Hadiza, 'yan kudu idan suka samu 'yar Arewa, "yadda suke tarairayarmu abin kamar ba a duniyan nan ba. Ji suke kamar sun yi wata nasara babba."
Hadiza ta bayyana cewa rashin yin kishiya na daga cikin abubuwan da ya sanya yanzu 'yan matan Arewa suke auren 'yan kudu.
A cewar Maryam, "Maganar cewa sun iya rike mata haka take."
Ta yi karin bayani cewa soyayyar 'yan kudu ta sha bamban da ta 'yan Arewa.
Domin a can ana koya masu kula da gida, sabanin a Arewa da idan namiji na taimaka wa a gida, sai a rika yi masa wani irin kallo.
No comments